Ganduje ya nada Nasir Ado Bayero Sarkin Bichi

Nasir Ado Bayero

Asalin hoton, Instagrma/Nasir Ado Bayero

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya nada Alhaji Nasir Ado Bayero a matsayin Sarkin Bichi.

Shi ne Sarkin Bichi na biyu, kuma zai gaji dan uwansa Alhaji Aminu Ado Bayero wanda ya zama Sarkin Kano.

Kwamishina yada labarai na jihar Kano Malam Muhammad Garba ya tabbatarwa da BBC nadin.

Gabanin nadinsa a matsayin Sarkin Bichi, Nasir Ado Bayero shi ne Ciroman Kano, babbar sarauta ta 'ya'yan Sarkin Kano.

Ya kuma taba zama Turakin Kano hakimin Nasarawa.

Alhaji Nasir Hamshakin dan kasuwa ne, kuma duk da cewa ba shi ne babba a 'ya'yan Sarkin Ado Bayero ba, yana da matukar kima a wajen 'yan uwansa, har wasu suna daukansa tamkar uba.

Asalin hoton, Instagram/Nasir Ado bayero