Farashin man fetur ya yi mummunar faduwa a duniya

Barkewar cutar Coronavirus a kasar Chana ya yi mummunan tasiri kan farashin man fetur a kasuwannin duniya
Bayanan hoto,

Barkewar cutar Coronavirus a kasar Chana ya yi mummunan tasiri kan farashin man fetur a kasuwannin duniya

Farashin danyen man fetur ya yi mummunar faduwar da bai taba yin irinta ba cikin shekaru da dama a kasuwannin duniya.

Barkewar cutar Coronavirus a kasar China ya shafi yadda kasar ta ke sayen man a kasuwar duniya.

Bugu da kari jayayya tsakanin Saudiyya da Rasha, yasa man fetur din ya yi kwantai.

Farashin danyen man ya fadi da kashi talatin cikin dari sakamakon matakin da kasar Saudiyya ta dauka na kara adadin man da take fitarwa zuwa kasuwannin duniya.

Hakama kasa cimma matsaya kan farashi tsakanin kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta OPEC da Rasha ya sa man ya yi mummunar ruguzowa.

Masana tattalin arziki na ganin ya zama dole kasashen da ke da man su rage yawan wanda suke fitarwa kasuwannin duniya da nufin daga farashinsa.

Hakama wasu masanan sun yi gargadin cewa ba man fetur kadai ba, cutar Coronavirus ka iya gurgunta tattalin arzikin duniya ga baki daya.

Ana ganin rikitowar farashin man fetur din zai iya shafar tattalin arzikin kasashe da dama wadanda tattalin arzikin nasu ya dogara ga man fetur kamar Najeriya.

Rahotanni na cewa gwamnatin Najeriya tuni ta kafa kwamiti don yin nazari kan yiwuwar rage kasafin kudin 2020 na fiye da naira tiriliyan goma da kuma kara yawan man fetur da Nijeriya ke hakowa don samun damar aiwatar da ayyukan da ta shata.

Bayanan hoto,

Ana ganin rikitowar farashin man fetur din zai iya shafar tattalin arzikin kasashe da dama wadanda tattalin arzikin nasu ya dogara ga man fetur kamar Najeriya

Duk da haka ana nuna fargaba kan yawan kudin ruwa na bashin da kasar ke biya, abin da wasu ke cewa na iya sanyata sake neman bashi.

Ba a jima ba da majalisa ta amincewa gwamnatin Shugaba Buhari ciyo bashi na sama da dala biliyan ashirin da biyu.