Coronavirus: Mara lafiya ya tsere daga asibiti

Covid_19

Asalin hoton, Getty Images

Ma'aikatar lafiya a Zimbabwe ta tabbatar da cewa wani mutum da ake zargin yana dauke da coronavirus ya tsere daga asibiti kafin a yi masa gwaji.

Cikin wata sanarwa, ma'aikatar ta ce mutumin mai shekara 26 ya shiga kasar a watan Fabrairu daga Thailand kuma ya fara zazzabi da atishawa.

A cewar sanarwar, bayan da mutumin ya tsere an bi shi gidansa don kamo shi amma ba a yi nasara ba kuma an bukaci jami'an 'yan sanda su nemo shi.

Kawo yanzu dai, alkaluma sun nuna cewa an samu masu dauke da cutar 100 a fadin Afirka.

Su ne:

  • Masar - 55
  • Algeria - 20
  • Afirka ta Kudu - 7
  • Tunisia - 5
  • Senegal - 4
  • Maroko - 2
  • Kamaru - 2
  • Burkina Faso - 2
  • Najeriya - 2
  • Togo - 1

Masar ce kasar da ta fi samun yawan masu dauke da cutar a nnahiyar Afirka.

Kawo yanzu a fadin duniya cutar ta kama kusan mutum 100,000 kuma ta kashe sama da 3,000 a China kawai.

Cutar ta billa a manyan kasashen duniya kamar Amurka da Burtaniya da Italiya.