An sauya wa Sarki Sanusi matsuguni daga Kauyen Loko

Bayanan bidiyo,

Tashin jirgin da ya dauki sarki Muhammadu Sanusi daga kauyen Loko

Wakilan BBC da suka kai ziyara kauyen Loko da ke jihar Nasarawa a Najeriya, inda aka fara kai Sarki Muhammadu Sanusi II bayan sauke shi daga sarautar Kano ranar Litinin, sun tabbatar da cewa an dauke shi daga garin don sauya masa wajen zama.

A lokacin da wakilan namu suka isa garin, sun ga jirgi mai saukar ungulu da ya dauki Sarkin zuwa inda ake kyautata zaton garin Awe ne, na jihar ta Nasarawa.

Tawagar BBC ta isa Loko da misalin karfe 1.40 na rana.

"Muna shiga garin daf da makarantar sakandaren da ake fara iskewa sai muka ga mutane sun yi cincirindo suna kallon jirgi mai saukar ungulu na rundunar 'yan sandan Najeriya yana tashi.

"A nan muka tambayi abin da ke faruwa aka kuma tabbatar mana da cewa tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II aka dauke za a mayar da shi garin Awe duk dai a cikin jihar Nasarawan," in ji Yusuf Yakasai na BBC.

Sai dai tun da fari Sarkin ya isa kauyen Loko da asubahin ranar Talata kuma an sauke shi a gidan limamin kauyen.

Wakilan namu sun ce Loko kauye ne sosai, kuma "Sarkin garin Alhaji Abubakar ya ce mana su da kansu ba su ga cancantar ajiye Sarki Sanusi II a garin ba, kasancewarsa karami kuma babu wutar lantarki babu abubuwan more rayuwa da zai bukata ko suka dace da shi."

"Kuma gaskiya hanyar zuwa garin ma ba ta da kyau sosai don mun shafe fiye da sa'a biyu daga garin Lafia zuwa can," in ji Yusuf.

Sarkin garin ya tabbatar wa da BBC cewa da ma an gaya musu za a kai Sarki Sanusi II shi ya sa ma suka tayar da aikin gaggawa na wajen da zai zauna, amma bai gaya musu takamaimai lokacin da aka gaya musu din ba.

Bayanan hoto,

Fadar Sarkin Loko

Alhaji Abubakar Sarkin Loko ya kuma ce babu wata alama ta damuwa tattare da Sanusi a yayin da ya ga irin garin da aka kai shi, "don har ya samu barci sosai cikin nutsuwa."

Abokan aikin namu sun samu sahihan bayanai cewa da safiyar Talata gwamnan Nasarawa da sarakunan gargajiya na jihar sun yi wani taro domin tattaunawa kan dauke Sarki Sanusi II daga Loko a sauya masa garin zama.

Alamu dai sun nuna cewa dama can an shirya Loko za a kai tsohon sarkin. Sannan ana ganin gwamnatin Nasarawa ta dauki matakin dauke shi ne don ganin wajen bai dace da shi ba.

Loko dai shi ne garin da ke kan iyakar jihar Nasarawa da Binuwai. Babu wuta ba ruwan sha mai kyau ba hanya mai kyau, babu sabis din kamfanonin waya sai daya tal.

Karin labaran da za ku so ku karanta: