Coronavirus: BBC ta amsa tambayoyin da kuka aiko

 • Fauziyya Kabir Tukur
 • BBC Hausa, Abuja
Coronavirus

Asalin hoton, Getty Images

Shekarar 2020 ta zo da wani babban al'amari wanda ya dauki hankalin duniya baki daya- wato sabuwar kwayar cuta ta coronavirus da ta bullo daga Wuhan, babban birnin lardin Hubei na kasar China wadda ke haifar da cuta mai suna covid-19.

Cutar ta bulla ne a watan Disambar 2019 amma kawo yanzu ta zama annobar da gaba daya duniya ke kokarin yaki da ita.

Daga farko da ta fara bayyana, likitoci a birnin Wuhan sun yi tunanin mura ce mai zafi ke kama mutanen saboda yadda alamominta ke kama da na mura.

Amma daga baya, da cutar ta fara yaduwa ne aka fahimci cewa wata sabuwar cuta ce da take shafar numfashi.

Bullarta ke da wuya, kasashen duniya suka fahimci cewa ta zama annoba saboda yadda take saurin yaduwa a tsakanin mutane.

Haka kuma, Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ayyana ta a matsayin wata annoba da ta addabi kasashen duniya baki daya.

Kawo yanzu, coronavirus ta yadu zuwa kasashen duniya sama da 160 kuma ta kashe mutum fiye da 14,000.

Haka kuma, a fadin duniya sama da mutum 300,000 ke dauke da cutar a yanzu, kuma mafi yawansu a wajen China suke.

Wasu na iya yin mamaki, ganin cewa cutar ta bulla a China kuma ta yi mummunar barna saboda lokaci da aka dauka kafin a fahimci irin cutar.

Nahiyar Turai ta kasance cibiyar annobar coronavirus kuma yawan masu dauke da cutar na karuwa a kasashen nahiyar da dama.

Ga amsoshin tambayoyin da kuka aiko mana kan cutar ta coronavirus ko covid-19.

Mene ne silar bullar coronavirus kuma a ina ta samu sunanta? Tambaya daga Muhammad Adam Jeri da Abubakar Yesso da Abubakar Saminu Agala da wasu da dama

A cewar Hukumar lafiya ta Duniya, WHO, Coronavirus wani gungun kwayoyin cutane da ake kira 'virus' da ke iya haifar da rashin lafiya ga mutane da dabbobi.

A cikin mutane, rabe-raben coronavirus da yawa na janyo cutukan numfashi kamar mura da kuma munanan cutukan numfashi kamar MERS da SARS da kuma sabuwar cutar numfashi ta coronavirus da aka gano kwanan nan, wacce take janyo cutar COVID-19.

Ana tunanin wannan sabuwar cutar ta coronavirus ta samo asali ne daga wata kasuwar sayar da naman dabbobin dawa da aka haramta sayarwa a Wuhan.

Wato dai cutar ta samo asali ne daga naman dabbobi.

Duk da cewa an sha ambato naman jemagu a matsayin asalin cutar, babu tabbas a kan hakan kuma ana ci gaba da bincike.

Mene ne alamomin cutar coronavirus kuma kwanan nawa take yi kafin ta bayyana a jikin mutum? Tambaya daga Annas Annur Sheka da Ahmd Muhammad da Noura Inoussa da Abdoul Hadi Niger

Asalin hoton, Getty Images

Cutar coronavirus na shafar huhu don haka ake ce mata cutar numfashi.

Alamominta na farawa ne da zazzabi, sai tari (marar majina) ya biyo baya daga nan kuma sai mai dauke da cutar ya ji shan numfashi na yi masa wahala.

Alamominta na farko-farko kan yi kama da alamomin mura da aka saba gani yau da kullum, sai dai ita coronavirus na zuwa ne da zazzabi mai zafin gaske da nauyin kirji ko ciwon hakarkari da shan numfashi da kyar.

Kwayar cutar na shiga jiki ne idan wani mai dauke da ita ya yi tari a kusa da mutane, sai kwayoyin cutar su bazu a kan teburi ko hannun kofa ko a fuska ko hannun mutanen da ke kusa.

Daga nan sai ta shiga makogaro ta kafar hanci ko baki ko ido, sai ta gangara zuwa huhu, daga nan kuma sai ta yi ta hayayyafa tana yaduwa har su kai ga shiga kwayoyin halitta da yawa da ke cikin jikin mutum.

Idan kwayar cutar coronavirus ta shiga jikin mutum, ta kan bayyana bayan kusan kwanaki biyar inda daga nan ne alamunta suke fara nunawa.

Amma Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ce kwayar cutar na iya zama a jikin mutum har tsawon mako biyu kafin a fara ganin alamominta.

Wasu masu bincike sun ce ta kan kai kwana 24 ma a jikin mutum sannan ta bayyana.

Dakta Nasiru Gwarzo wani masanin harkar lafiya ne a Najeriya, ya ce duk wanda ya yi tafiya zuwa wani yanki da cutar take, da ya koma gidansa dole ne ya killace kansa har sai ma'aikatan lafiya sun duba shi.

Asalin hoton, corona bbc

Ana warkewa daga cutar coronavirus? Tambaya daga Auwal Abdulkadir Olanse da Abdulkareem Wura

Wani binciken Hukumar Lafiya ta Duniya ya nuna cewa cikin mutum 56,000 da suka kamu da cutar covid-19:

 • Kashi 6 cikin 100 ne cutar da jefa su cikin halin rai kwakwai mutu kwakwai- wato cutar ta haifar masu da lalacewar huhu da dogon suma da lalacewar sauran kayan cikinsu da fadawa hadarin mutuwa.
 • Kashi 14 cikin 100 sun fusknaci matsaloli kamar gaza yin numfashi da haki.
 • Kashi 80 cikin 100 sun fuskanci alamomin cutar saisa-saisa kamar zazzabi da tari sannan wasu daga cikinsu sun fuskanci ciwon limoniya

Wannan na nuna cewa mafi yawan mutanen da za su ko kuma suka kamu da cutar covid-19 za su warke.

Bincike ya nuna cewa cutar kan shiga jikin wasu kuma ba za su fuskanci wasu alamomi ba, ko kuma su fuskanci kadan daga cikin alamominta.

Alkaluma sun nuna cewa mutum fiye da 300,000 ne suka kamu da cutar a duniya zuwa 19 ga watan Maris na 2020, amma kusan mutum 14,000 ne kawai cutar ta kasha.

Kuma mutum takwas cikin 10 na wanda cutar ta kama za su warke bayan fuskantar alamominta sama-sama.

Wakilin BBC kan harkokin lafiya, James Ghallager ya ce garkuwar jikin dan adam na aiki tukuru don yaki da cutar coronavirus don kuwa ta kan fahimci cewa wani abu (wato kwayar cutar) mai hadari ya tunkaro ta don haka sai ta aika wa sauran sassan jiki cewa wani abu marar kyau na shirin faruwa da su.

Daga nan ne garkuwar jiki take fitar da wani sinadari mai suna Cytokines, wanda ke ya zama kamar dakari ne a jikin. Wannan ne ke haifar da zazzabi da rashin karfi a jika ga mai fama da cutar.

Coronavirus na da magani, ana warkewa daga cutar? Tambaya daga Abdourazak da Maharazu Abbas da Khalid Khan

Dakta Gwarzo y ace "A halin yanzu babu magani ko riga-kafin cutar coronavirus amma ana nan ana bincike."

Amma BBC ta gano cewar wasu masu bincike sun samar da riga-kafi kuma sun fara gwada ta a jikin dabbobi da mutane. Idan suka yi nasara za a fara bayar da ita zuwa karshen shekarar nan.

Kwararru sun ce za a kwashe watanni da dama kafin a sani idan lallai riga-kafin za ta yi aiki.

Sai dai wani abin dubawa a nan shi ne, ko da an yi nasara riga-kafin ta yi aiki kafin shekara mai zuwa, samar da ita da yawa, yadda har za ta isa duka kasashen duniya jan aiki ne.

An yi wa wasu mutum hudu allurar riga-kafin a cibiyar bincike ta Kaiser Permanente da ke birnin Seattle a Washington din Amurka, a cewar kamfanin dillancin labarai na AP.

Ana warkewa daga cutar coronavirus ta hanyar bin dokokin da likitoci suka bayar kamar hutawa sosai da yawan shan ruwa da kula da tsaftar jiki da ta muhalli.

Idan mutum ya ji alamun cutar coronavirus, sai ya yi gaggawar sanar da ma'aikatan lafiya ta hanyar buga masu waya.

Asalin hoton, Getty Images

Amma Dakta Gwarzo ya ce kada mutum ya yi saurin zuwa asibiti don idan yana dauke da cutar zai iya cutar da mutaen da dama "ta hanyar yada ta ga ma'aiakatn lafiyar da saura marasa lafiyan da ke asibitin da wadanda zai gamu da su a hanya."

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce cutar COVID-19 ta fi wahalar da tsofaffi da mutanen da ke da wata cuta ta daban kamar hawan jinni ko ciwon zuciya ko ciwon huhu ko daji ko ciwon suga.

Don haka idan mutum na da isasshiyar lafiya kuma yana cin abinci mai gina jiki, zai yi wuya cutar ta durkusar da shi ko ta kashe shi.

Shin coronavirus na kama Musulmi da bakar fata da kananan yara? Tambaya daga Muhammad Sani da Sa'idu Gombe da Adamu Sulaiman da Ahmad Ado Ahmad da Alfani Baba

Cutar coronavirus tana kama mutane daga ko wane jinsi da kabila da addini da shekaru.

An samu bullar cutar a kasashen duniya sama da 160 kuma a duka kasashen nan akwai farar fata da bakar fata da manya da yara kanana da mabiya addinai daba-daban na duniya.

Kasar Saudiyya da Iran na daga cikin manyan kasashe musulunci da cutar ta bulla kuma kawo yanzu sama da mutum 1000 sun kamu da cutar a wadannan kasashe biyu hade.

Bullar cutar coronavirus a Saudiyya ne ma ya sa kasar ta dauki wasu tsauraran matakai don hana yaduwar ta.

Saudiyya ta hana 'yan sauran kasashen duniya da 'yan kasarta yin aikin Umra na wucin gadi, sannan ta killace dakin Ka'aba ta hanyar zagaye shi da wani shinge.

Hikimar yin hakan shi ne don hana yaduwar cutar ganin yadda ake cunkuso a wurin dawafi.

Mutum sama da 40 ne suka kamu da cutar coronavirus a Saudiyya kuma har a garin Makka an samu sama da mutum 20 da cutar. Amma an samu mutum daya da ya warke cikinsu.

A kasar Iran kuwa, sama da mutum 17,000 ne suka kamu da cutar ciki har da ministan lafiyar kasar Iran Hirirchi da mataimakiyar shugaban kasar Masoumeh Ebtekar.

Hukumar lafiya ta Duniya ta sanar cewa ita ce kasa ta uku a duniya da cutar ta fi shafa.

A Afirka, kawo yanzu cutar ta shiga kasashe sama da 30 kuma an samu 'yar Afirka ta farko da cutar ta kashe a Burkina Faso.

Haka kuma, a Najeriya ma an samu mutum takwas masu dauke da cutar kamar yadda Hukumar Kula da Yaduwar Cutuka ta kasa, NCDC ta sanar, kuma cikin wadannan mutane har da jaririya 'yar mako 6.

Don haka, cutar coronavirus na kama musulmi kuma tana kama bakar fata da kananan yara kuma ta na tasiri a yankuna masu zafi, akasin yadda wasu ke cewa.

Ya zan kare kaina daga kamuwa da cutar?

Asalin hoton, Getty Images

 • Abu mafi muhimmanci shi ne yawan wanke hannu sosai da ruwa da sabulu. A kwashe tsawon a kalla dakika ashirin ana wanke tafukan hannu.
 • Idan za a yi tari ko atishawa a rufe baki da hanci da tolifefa ko hankici.
 • Za a iya gujewa kamuwa da cutar idan aka daina taba fuska da hannuwan da ba a wanke ba sannan a guji mu'amala da mutanen da ke da cutar.
 • Rage shiga cunkoson mutane, kamar dakin taro ko motar haya ko jirgin kasa ko na sama.
 • Kwararru a fannin lafiya sun ce takunkumin fuska ba ya ba da cikkiyar kariya daga cutar.
 • Jefa tolifefar da aka share hanci da ita a kwandon shara.
 • A daina yin musabiha da mutane saboda cutar na rayuwa a tafukan hannun mutane.
 • A tabbata an dafa nama da kwai sosai kafin a ci.

Idan kana kula da marar lafiya mai dauke da cutar, ga hanyoyin da za ka bi don kare kanka:

Kada ka kusanci mai dauke da cutar, ka bar tsakanin a kalla mita 2 da shi ko ita, a cewar Hukumar Lafiya ta Ingila.

A takaita lokutan da ake zama tare a matsattsen wuri kamar dakin girki kuma a tabbata iska na kewayawa a duka dakunan gidan. Zai fi kyau su killace kansu a daki daya su kadai.

Mai fama da cutar zai yi amfani da tawul da zannuwansa daban da sauran mutanen gidan.

Idan da hali a ware masu makewayinsu, idan kuma babu hali da zarar sun yi amfani da makewayin sai an wanke shi tas.

A jira awa 72 kafin zubar da abubuwan da suka yi amfani da su kamar tolifefa ko audugar mata bayan an kulle su a jakar leda.

Yaushe coronovirus zata kare a fadin duniya? Tambaya daga Dauda Sani Kunya

Asalin hoton, Getty Images

Wakilin BBC a fannin lafiya, James Ghalleger ya ce babu takamaimiyar amsa kan wannan tambayar amma akwai hanyoyi uku kwarara da za a iya bi don kawo karshen cutar:

 • Rigakafi- idan komai ya tafi yadda ake so ba za a samu rigakafi ba sai nan da a kalla wata 18
 • Samun mutane da yawa da garkuwar jikinsu ta yi karfi saboda harin kwayar cutar- wannan zai dauki a kalla shekara 2 kuma akwai ayar tambaya a kan tasirin wannan matakin. Sauran na'ukan coronavirus kan kashe garkuwar jiki kuma wasu kan yi shi fiye da sau daya a rayuwarsu.
 • Sauya halayyarmu ta din-din-din

Sai dai ko da yawan masu dauke da cutar ya fara raguwa nan da wata uku masu zuwa, to hakan fa ba yana nufin an kawo karshen matsalar ba ne.

Za a dauki tsawon lokaci kafin annobar ta gama tafiya - watakila ma shekaru.

Abin da kasashe ke bukata shi ne ''daukar matakin fita daga wannan kangi'' - hanyar da za a dage wadannan matakan a koma rayuwa yadda aka saba.

Amma ga alama coronavirus ba ta shirya tafiya ba a yanzu.

Idan aka dage matakan takaita walwalar jama'a da ke dakile yaduwar cutar, to kuwa lallai za a samu karin mutanen da za su kamu.

Ana iya kamuwa da cutar fiye da sau daya? Tambaya daga Alajin Ngari da AbdurRahman Muhammad Yelsu

Wannan tambaya ce da har yanzu ba ta da tsayayyar amsa saboda kan kwararru ya rarrabu inda wasu ke ganin cewa idan mutum ya kamu da cutar sau daya ba ya iya sake kamuwa saboda jiki na kafa garkuwa da ita.

Yayin da daya bangaren ke ganin cewa wasu na iya sake kamuwa da cutar.

Ana ci gaba da bincike a kan wannan batu kuma ko a Burtaniya, Sir Patrick Vallance, babban mai mai wa gwamnati shwara kan kimiyya da farfesa Chris Whutty, babban mai bai wa Fairanminista Boris Johnson shawara, sun ce zai yi wuya wanda ya taba yin cutar ya sake kamuwa.

Daga karshe, akwai abubuwan da yin su ba zai kare ka daga kamuwa da coronavirus ba kuma suna iya cutar da kai, kamar yadda WHO ta wallafa a shafinta:

 • Shan taba
 • Sanya takunkumin fuska da yawa a lokaci guda
 • Shan magungunan 'antibiotics' ba tare da sanin likita ba.