Coronavirus: Yadda matasa suka yi ganganci da rayuwarsu a Amurka

Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Gungun matasa a Amurka sun je wata liyafa a jihar Florida duk da shawarwarin da hukumomi suka bayar na na takaita taruwar mutane da yawa don hana yaduwar cutar a kasar.

Hukumomin lafiya na shawartar mutane da kada su yi taron mutum sama da 10 a lokaci daya domin hana yaduwar cutar a cikin al'umma.

Shugaba Trump ya yi kira ga matasa da su sauya tsarin rayuwarsu domin kada su dauki cutar su yadawa 'kakanninsu da iyayensu'.