Coronavirus: Adadin masu cutar ya kai 46 a Nigeria

Kwayar cutar covid-19 Hakkin mallakar hoto Getty Images

Hukumar hana yaduwar cutuka ta Najeriya NCDC, ta ce adadin wadanda suka kamu da coronavirus a Najeriya ya kai 46, bayan wasu mutum sun sake kamuwa da ita.

Daya a Jihar Legas yake, shi kuma dayan a Jihar Osun - duka a yankin kudancin kasar - in ji NCDC.

Da yammacin ranar Talata hukumar ta bayyana hakan, inda ta ce dukkaninsu sun shigo Najeriya ne a cikin mako guda da ya gabata.

"Ya zuwa misalin karfe 7:00 na yamma (Talata) mutum 46 ne suka kamu da Covi-19 a Najeriya," kamar yadda NCDC ta wallafa a Twitter.

Jihohin da aka samu bullar Covi-19 a Najeriya

  • Legas- 30
  • Abuja - 8
  • Ogun- 3
  • Ekiti- 1
  • Oyo- 1
  • Edo- 1
  • Bauchi-1
  • Osun-1
  • Jumulla - 46

Tuni dai biyu daga cikin 46 din suka warke, yayin da mutum guda kuma ya mutu.

Ci gaba da yaduwar da coronavirus ke yi ya sanya gwamnatin tarayyar Najeriyar da ma gwamnatocin jihohi daukar matakan dakile yaduwarta.

Daga cikin matakan da aka dauka a kasar har da dakatar da sauka da tashin jiragen sama na kasa da kasa.

Har wa yau, Najeriya ta dakatar da dukkan zaman shari'a da kotunan kasar ke yi, sai dai a kan lamari na gaggawa saboda fargabar cutar COVID-19.

Ita kuwa gwamnatin jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriyar, haramta kai ziyara sansanin 'yan gudun hijira ta yi na tsawon mako hudu.

A jihar Kano kuwa, gwamnatn jihar ce ta haramta dukkan wani taron jama'a a fadin, a wani matakin dakile cunkoson al'umma domin kauce wa kamuwa da cutar.

Zamfara kuwa umarnin rufe dukkan hukumomin gwamnatin jihar ta yi domin kauce wa kamuwa da coronavirus.

Gwamnatin jihar Neja kuwa ta sanar da sanya dokar hana fita daga karfe takwas na safe zuwa takwas na dare.

Labarai masu alaka