Coronavirus: Mene ne barin tazara da killace kai?

Wata mata na motsa jiki a bakin ruwa a London Hakkin mallakar hoto Getty Images

An ba da umarnin rufe shagunan da ke sayar da abubuwa marasa muhimmanci tare da dakunan karatu da filayen wasannin yara da wuraren motsa jiki da wuraren ibada.

An haramta bukukuwan aure amma ba a hana yin jana'iza ba.

An hana taron mutanen da suka haura mutum biyu da ba 'yan gida daya ba.

Mutane na iya motsa jiki sau daya a rana su kadai ko tare da wani dan gidansu.

Sauran abubuwan da aka amince a yi a waje su ne:

 • Fita sayayyar kayan amfani na yau da kullum kuma shi ma a saya dai-dai-wa-daida
 • Zuwa asibiti ko kuma kai wani asibiti
 • Zuwa wajen aiki ko dawowa daga aiki idan ya zama dole

Me ya kamata in yi?

Idan har ya zama dole mutane su fita don sayen abinci misali, dole ne su bar tazarar sama da mita 2 daga sauran mutane.

An bai wa Shagunan sayar da gahawa da mashaya da gidajen abinci da wuraren yin fati da silma da wuraren motsa jiki umarnin rufewa. Wannan mataki ne na barin tazara don hana mu'amala a inda bai dace ba.

An ba da umarnin cewa mutanen da ke da alamomin mura- kamar tari marar majina da zazzabi- su killace kansu a gida don gudun shafa wa wasu.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Me ya sa barin tazara ke da muhimmanci?

Barin tazara na da muhimmanci saboda coronavirus na yaduwa ne idan mai dauke da cutar ya yi tari kuma kwayoyin cutar suka fito daga bakinsa suka shiga iska.

Ana iya shan kwayoyin cutar ta isak ko idan suka sauka a kan wani abu kuma aka shafi abun da tafin hannu, sannan a taba fuska ba tare da wanke hannuwan ba.

Idan mutane bas u dade a kusa da juna ba, akwai yiwuwar ba za su dauki cutar daga wani ba.

Idan da hali, kada ku fita ko da sayen abinci ne ko kuma sauran kayan amfani. Gara ku kira waya a kawo maku kayan da kuke bukata har gida idan ana yin haka a kasarku.

Wasu kasashen fa?

Matakan da wasu kasashen suka dauka sun fi na Burtaniya tsauri don tabbatar da cewa mutane sun bar tazara a tsakaninsu.

 • An hana fita ko ina a gaba daya Italiya tun ranar 9 ga watan Maris
 • A karshen makon da ya wuce, a yankin Lombardy na Italiya an hana motsa jiki idan ba a kusa da gidanka ba
 • Jihohin Amurka da dama sun sa dokoki don hana miliyoyin mutane fita
 • A Sifaniya, an haramta wa mutane fita daga gidajensu har sai idan za su sayi abinci ko magani ko zuwa aiki
 • A Belgium, an rufe duka shaguna masu sayar da kayan da bas u da muhimmanci kuma an ce wa mazauna kasar su zauna a gida har sai a kalla 5 ga watan Afrilu. Mutum na iya yin dan tattaki da motsa jiki amma dole ya bar tazara. An kuma hana duka nau'I na taruka.
 • Faransa ta dakatar da duka ayyuka a kasar tsawon kwanaki 15. Sama da 'yan sanda 10,000 ne suke tsaron tituna don tabbatar da cewa an bi doka, sannan duk wanda ya karya dokar ana cin tararsa Euro 135.
 • A Jamus an hana taron sama da mutum biyu. A Bavaria, wata jiha a Jamus, an hana duka mazauna jihar fita ko da nan da can ne.
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mutane na samar da tazara a tsakaninsu

Mene ne killace kai?

Killace kais hi ne zama a gida ba tare da an fit aba sai don motsa jiki. Kada a je aiki ko makaranta ko wani wurin taron jama'a a wnnan lokaci.

Waye ya kamata ya killace kansa?

Duk wanda ke da wata alama ta coronavirus- zazzabi da zafinta ya kai maki 37.8C, tari ba kakkautawa da yin numfashi da kyar- da kuma duk wani da ke zaune a gida daya da wanda ke da alamun cutar.

 • Idan kai kadai kake zama a gidan, dole ka ci gaba da zama a gida tsawon kwana 7 daga ranar da ka fara jin alamunta
 • Idan kai ko wani da ke zama da kai ya fara jin alamu, dole ne duka gidan kowa ya killace kansa tsawon mako 2 don tabbatar da ko ana dauke da ita ko akasin haka
 • Idan wani daga cikinku ya kamu a wannan lokaci, daga ranar za su fara kirga ranakun killace kansu tsawon kwana 7. Misali, daga rana ta 3 zuwa ta 10- lokacin ne mutumin zai daina killace kansa. Ba za a sako daga farko ba idan wani a gidan ya kamu
 • Amma duk wanda ya fara rashin lafiya a rana ta 13, zai kirga ranar a matsayin rana ta farko ta killace kansa saboda rashin lafiyar ba don ganin alamu ba- hakan na nufin zai kwashe tsawon kwana 20 a gida ba fita.
 • Wanda ke da alamun cutar zai zauna a daki mai iska kuma a bude tagogi, sannan ya ware kansa daga sauran mutanen gidan.

Ana ba da shawarar cewa duk wanda ya ji alamu ya kula da kansa a gida tukunna har sai ya ji yana bukatar taimako kafin ya buga wa jami'an lafiya waya.

Wa ye bai kamata ya fita ba gaba daya?

Akwai mutane miliyan daya da rabi a Burtaniya da ke fama da cutuka masu hadari kuma hukumar lafiya za ta neme su ta bas u shawarar kada su fita sai nan da akalla mako 12.

Sauran mutane da ke zama a gida daya da su da masu bas u kula na iya fita matsawar za su kula da ba da tazara.

 • Wadanda suke cikin wannan kaso sun hada da:
 • Masu fama da ciwon daji ko wane iri
 • Wadanda aka yi wa dashen wani kayan ciki
 • Masu dauke da wasu cutuka na gado
 • Masu fama da cutukan numfashi
 • Masu shan magungunan da ke shafar garkuwar jiki
 • Masu ciki da ke da ciwon zuciya
 • Gwamnatin Burtaniya ta ce za ta yi aiki da kananan hukumomi da manyan kantuna da jami'an tsaro wajen samar da abinci da magunguna.
Hakkin mallakar hoto Getty Images

Me zai faru idan wani mai dauke da mummunar cuta na zaune da kai a lokacin da kake killace kanka?

Ka bar tazarar a kalla mita 2 daga marar lafiyar (misali mai ciki ko tsoffi ko masu wata cuta da suka dade suna fama da ita) a lokacin da kake killace kanka.

A takaita lokacin da ake zama tare a wuri guda kamar dakin girki, kuma a bude tagogin duka gidan. Idan za a iya marar lafiyar ya ci abincinsa a daki shi kadai

Marar lafiya ko mai ciki ko tsoffi su yi amfani da tawul dinsu na daban da sauran 'yan gida. Idan da hali, a ware masu makewayinsu. Amma idan babu hali, sai a wanke makewayin duk lokacin da suka yi amfani da shi.

Ya kamata, masu zama da wanda ya killace kansa su wanke hannunsu a-kai-a-kai ta hanyar amfani da sabulu da ruwa tsawon dakika 20- musamman bayan an yi mu'amala da su.

An kulle abubuwan amfani kamar toli fefa a jakar leda biyu sannan a ajiye su tsawon kwanaki 4 kafin a sa a kwandon shara.

Labarai masu alaka