Sadio Mane zai koma Real Madrid

Sadio Mane

Dan wasan Liverpool dan kasar Senegal Sadio Mane, mai shekara 27, zai koma Real Madrid kuma idan Mohamed Salah ya bar kungiyar zai fi zama alheri a gare ta, a cewar tsohon dan wasan Liverpool Mohamed Sissoko. (Sun)

Har yanzu dan wasan Manchester City da Ingila Raheem Sterling, mai shekara 25, yana shaukin Liverpool duk da matsalolin da suka sanya ya koma City. (Sky Sports)

Liverpool, Manchester City da kuma Arsenal suna zawarcin dan wasan Schalke dan kasar Jamus mai shekara 18 Malick Thiaw wanda farashinsa ya kai £6.9m. (Mail)

Manchester United na ci gaba da yin fatan cewa dan wasan Faransa mai shekara 27, Paul Pogba, ba zai bar Old Trafford ba inda take shakka kan ko za a samu babban kulob a Turai da zai iya sayensa. (ESPN)

Real Madrid na son sayo dan wasan Borussia Dortmund Erling Braut Haaland, mai shekara 19, a kakar wasa mai zuwa, ko da yake su ma Manchester United da Tottenham suna son dauko. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Chelsea ta ware £23m don dauko dan wasan Getafe dan kasar Spain Marc Cucurella, mai shekara 21, a bazara. (Diario Sport - in Spanish)

Kazalika Chelsea na son sayo dan wasan Ajax dan kasar Argentine Nicolas Tagliafico, mai shekara 27, bayan ta yi watsi da yunkurinta na dauko dan wasan Leicester Ben Chilwell. (Calciomercato via Daily Express)

Dan wasan Manchester United mai shekara 30 wanda Roma ta yi aronsa, Chris Smalling, zai iya komawa kungiyar din-din-din idan Manchester United ta sayo dan kasar Senegal Kalidou Koulibaly daga Napoli. (Gazzetta dello Sport via Football Italia)

Ranar Laraba za a kawo karshen killacewar da aka yi wa 'yan wasa da ma'aikatan Juventus, kuma za a kyale su su bar fita daga gidajensu. Amma za a ci gaba da killace 'yan wasa irin su Daniele Rugani, Blaise Matuidi da kuma Paolo Dybala, a yayin da suke ci gaba da murmurewa daga coronavirus. (Gazzetta dello Sport)

Dan wasan Crystal Palace Wilfried Zaha ya yi kira ga masu gidajen hayan da babu kowa a cikinsu su bari ma'aikatan lafiyar da ke aiki don yakar coronavirus a London su rika amfani da su. (Evening Standard)

Labarai masu alaka