Coronavirus: Sakamakon gwaji ya nuna Osinbajo ba shi da cutar

Osinbajo Hakkin mallakar hoto Getty Images

Mai bai wa shugaban Najeriya, shawara kan harkokin siyasa, Ujudu Babafemi ya ce sakamakon gwaji guda 10 da aka yi wa mataimakin shugaban, Farfesa Yemi Osinbajo sun nuna ba ya dauke da kwayar cutar coronavirus.

A shafinsa na Facebook, Babafemi ya ce baya ga mataimakin shugaban kasar, dukkan masu taimaka masa ma sun tsira daga kamuwa daga cutar.

Kafin nan dai mai taimaka wa farfesa Osinbajo, kan yada labarai, Laolu Akande ya wallafa cewa mataimakin shugaban na killace kansa kamar yadda hukumar lafiya ta duniya ta nuna.

Ko a jiya ma sai da Laolu Akande ya wallafa wani hoton mataimakin shugaban yana gudanar da harkokinsa ta hanyar intanet sanye da takunkumin kariya.

Wannan dai na zuwa ne kwanaki biyu bayan da ta bayyana cewa shugaban ma'aikata a fadar shugaban Najeriya, Abba Kyari da gwamnan Bauchi, Bala Muhammad sun kamu da cutar ta coronavirus.

Ana kyautata zaton cewa mataimakin shugaban na Najeriya, Yemi Osinbajo ya gana da mutanen guda biyu a tsawon kwanakin da suka gabata.

Labarai masu alaka