Coronavirus: Ali Nuhu da abokan aikinsa 'ba sa cikin hatsari'

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Coronavirus: Ali Nuhu 'ba ya cikin hatsari'

Latsa hoton da ke alamar lasifika ta sama don sauraron hira da Ali Nuhu:

Tauraron fina-finan Kannywood, Ali Nuhu, ya ce hukumomin lafiyar Najeriya sun shaida musu cewa shi da abokan aikinsa ba sa cikin hatsarin kamuwa da coronavirus.

Ali Nuhu ya shaida wa BBC cewa hukumar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC ta ce ba a bukatar yi musu gwajin cutar.

Batun yi musu gwajin ya taso ne bayan kiran da gwamnatin jihar Lagos ta yi cewa duk wanda ya halarci bikin karrama jarumai da aka gudanar a birnin na Lagos ya je a yi masa gwajin coronavirus saboda ta gano cewa wani mai dauke da cutar ya halarci bikin.

Ali Nuhu da wasu 'yan Kannywood biyar na cikin taurarin da suka halarci bikin ranar Asabar 14 ga watan Maris.

Sauran 'yan Kannywood din da suka je bikin su ne: Ado Gwanja da Abubakar Maishadda da Hassan Giggs da kuma wani mutum daya.

Sai dai a tattaunawarsa da BBC ranar Laraba, tauraron ya ce hukumar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya ta gano cewa mutumin da ake zargi yana da cutar ba shi da ita.

'Ruwa ta sha'

"Sun ce mu kebe kanmu za su zo su dauki samfurinmu kuma har yanzu da na yi maka magana basu zo sun dauki samfurin namu ba... su kansu sun gane cewa wannan maganar karya ce," in ji tauraron.

Ya kara da cewa jami'an hukumar NCDC sun shaida musu cewa su ci gaba da harkokinsu ba tare da wata fargaba ba, yana mai cewa "sun gaya mana idan mun ji wani abu da yake damunmu mu sanar da su."

Ya zuwa yanzu dai fiye da mutum 40 ne suka kamu da cutar a Najeriya, ciki har da shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar, Malam Abba Kyari da gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed.

A karon farko tun bayan barkewar cutar a Najeriya, an samu mutum daya ya mutu sanadiyyar ta ranar Litinin ko da yake mutum biyu sun warke.

Hakkin mallakar hoto Instagram/realabmaishadda
Image caption Daga dama zuwa hagu: Abubakar Maishadda, Ali Nuhu, Ado Gwanja da Hassan Giggs a wurin bikin karrama taurarin fim a Lagos