Covid-19: Mutum shida sun warke daga coronavirus a Lagos

Babajide Sanwo-Olu

Asalin hoton, Twitter

Mai magana da yawun gwamnan jihar Legas, Tunde Ajayi, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa an samu mutum shida da suka warke daga cutar coronavirus.

Hukumar NCDC dai ta sanar da cewa akwai masu coronavirus 32 a jihar Legas.

Yanzu kenan mutanen da ke dauke da cutar a jihar ta Legas sun kama 26.

Wannan dai na zuwa ne 'yan sa'o'i kadan kafin gwamnatin jihar ta sanar da kudirinta na yin feshi a ilahirin jihar.

Gwamnan jihar, Babajide Sanwo-Olu ne ya wallafa hakan a shafinsa na Twitter, inda ya ce jihar za ta raba kayan feshin magani zuwa lungu da sako na jihar a ci gaba da yaki da annobar coronavirus.

Jihar ta Legas dai ita ce gaba-gaba wajen yawan masu dauke da cutar coronavirus a Najeriya, inda daga cikin mutum 51 da hukumar NCDC ta sanar, 32 daga jihar ne.

Ya zuwa yanzu dai mutum 43 ne ke fama da cutar a Najeriya.

Asalin hoton, Babajide Sanwo-Olu's Twitter