Coronavirus: Amurka za ta bai wa kowanne dan kasa tallafin dala 1,200

Donald Trump

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mutanen da coronavirus ta kashe a Amurka sun kai 1,000

'Yan majalisar Amurka sun amince da dalar Amurka tiriliyan 2 a matsayin tallafin rage radadin cutar coronavirus, wanda ya hada da bai wa dukkan 'yan kasa matasa dala 1,200 kyauta (sama da naira 400,000).

An samu tsaiko yayin kada kuri'ar amincewa da kudirin dokar sakamakon rikici tsakanin 'yan jam'iyyar Democrats da Republican a kan alfanon da marasa aikin yi za su samu a cikin kudirin.

Daga cikin abin da kudirin ya kunsa akwai bai wa kusan kowanne baligi dala 1,200 a matsayin tallafi sannan kuma a taimaka wa masu matsakaitan kasuwanci biyan albashin ma'aikatansu.

Wadanda suka mutu a Amurka sakamakon cutar sun kai 1,000 sannan kuma akwai kusan 70,000 da aka tabbatatar suna dauke da cutar.

A duniya baki daya, fiye da mutum 21,000 ne suka mutu tun daga sanda annobar ta barke a yankin Hubei na China a watan Disamba. Wadanda suka kamu kuwa sun kusa rabin miliyan.

Kudancin Nahiyar Turai ce cibiyar annobar a yanzu, inda kasashen Sifaniya da Italiya ke samun daruruwan mamata a kullum.

Abin da dokar ta kunsa

Yarjejeniyar da aka cimma tsakanin shugabannin Democrats da Republican ta kunshi haraji da rance da kudin da za a bai wa asibitoci da kuma tanadin kayan ceto.

Kudirin dokar mai shafi 900 ya kunshi zunzurutun kudin da ya kai kusan rabin kasafin kudin kasar na shekara.

Daga ciki akwai:

  • Biyan Amurkawa dala 1,200 wadanda ke samun dala 75,000 a shekara ko kasa da haka da kuma karin dala 500 ga duk yaro daya - ga masu 'ya'ya
  • Fadada kudin tallafi ga marasa aikin yi da zai hada da biyan mutanen da ke sana'ar hannu ko kuma suke aikin kwantaragi
  • Tallafa wa kamfanoni da dala biliyan 500 musamman wadanda suka fi jigata kamar na jiragen sama
  • Bayar da rancen dala biliyan 350 ga kananan 'yan kasuwa
  • Bayar da dala biliyan 100 ga asibitoci da kuma sauran ma'aikatu masu alaka da ke kan gaba a yaki da cutar