Coronavirus: Lokaci na neman kurewa Najeriya - Lai Mohammed

Lai Mohammed

Asalin hoton, Getty Images

Gwamnatin Najeriya ta ce lokaci yana neman kurewa kasar a yunkurin da take yi na yaki da cutar covid-19.

Ministan watsa labaran kasar Lai Mohammed ne ya bayyana haka a taron manema labaran da ya gudanar ranar Alhamis.

Ya nuna matukar rashin jin dadinsa game da bijirewar da 'yan kasar suke yi ga umarnin da gwamnati ta yi musu na daukar matakan kare kai daga kamuwa daga cutar.

Ministan ya ce gwamnati ta bukaci 'yan Najeriya su rika bai wa juna tazara wurin mu'amala da shaida wa hukumomin lafiya idan sun ga alamomin cutar a jikinsu da yin gwaji da kuma killace kansu.

"Amma zancen gaskiya lokaci yana neman kure mana. Idan bamu dauki matakan gaggawa na tursasa wa mutane bin umarnin da na zayyana ba, ganin cewa muna da karancin lokaci na dakile wannan annoba, to za a samu gagarumar karuwar wadanda za su kamu da ita", a cewar Lai Mohammed. Ya kara da cewa gwamnatin Najeriya ta dauki matakai daban-daban don dakile cutar, cikinsu har da haramta wa jiragen saman kasashen waje shiga Najeriya da rufe kasuwanni da ofisoshi da makarantu da sauransu.

Ministan ya yi wannan kira ne a yayin da aka samu karuwar mutanen da suka kamu da coronavirus a kasar.

Hukumar hana yaduwar cutuka ta Najeriya NCDC ta ce an samun karin mutum 14 da suka kamu da cutar covid-19.

A sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter ranar Alhamis da daddare, hukumar ta ce 12 daga cikinsu a Lagos suke yayin da biyu kuma suke Abuja.

Ta kara da cewa an gano shida daga cikinsu ne a wani jirgin ruwa, uku kuma matafiya ne a tsakanin jihohin kasar, daya kuma wanda ya yi mua'amala da mutumin da aka tabbatar yana da cutar ne.