Amurka ta zama kasa mafi yawan masu coronavirus a duniya

Coronavirus

Asalin hoton, Getty Images

Amurka a yanzu ta zarce hatta kasar China a yawan masu fama da annobar coronavirus, inda Amurkawa 82,404 aka tabbatar sun kamu, a cewar kididdigar Jami'ar Johns Hopkins.

A cewar kididdigar da Jami'ar Johns Hopkins ta fitar, Amurka ya zuwa yanzu tana da mutum sama da dubu tamanin da biyu da dari hudu da suka kamu da cutar sabanin China da ke da yawan mutanen da ba su haura dubu tamanin da biyu masu fama da annobar ba.

Italy kuma tana da mutum dubu tamanin da dari biyar da suka kamu da cutar.

Wakilin BBC ya ce a yanzu Amurka ce cibiyar annobar coronavirus kuma sama da mutum dubu daya sun mutu sanadiyyar cutar a kasar.

Shugaba Trump a wani taron manema labarai ya yi watsi da sukar da ake yi kan rashin wadatattun kayan aiki inda ya ce gwamnatinsa ta gaji abin da ya kira 'rusasshen tsarin samar da abinci don bukatar gaggawa.''

A wata alama da ke nuna karin takurar da harkokin lafiyar Amurka suke fuskanta, wata ma'aikaciyar jinya mai kula da masu fama da cutar koronabairus a Oakland, cikin jihar Michigan, ta wallafa wani bidiyo, cikin kuka tana rokon Amurkawa su dauki wannan annoba da gaske.

Ta ce tsawon sa'a 13 da ta yi aiki a sashen da ake ba da matsananciyar kulawa a asibitinsu. "Ban san abin da ke faruwa ba" in ji kwararriyar wadda ba ta amince a ambaci sunanta ba.

Ma'aikaciyar jinyar ta ce a gaskiya, ta ji tamkar tana aiki ne a wani fage yaki.

"Gaba daya na kadaita daga sauran jami'an da muke aiki tare. Kayan aiki sun yi karanci, kayan likitanci da ake bukatar a kawo sun yi karanci, akwai karancin samun dauki daga likitoci, saboda su ma aiki ya sha musu kai kamar yadda ya sha mana."

A cewarta, tsawon sa'a 13 ta kula da lafiyar masu fama da annobar covid19 biyu da ke cikin mawuyacin hali kuma aka sanya musu na'urar tallafa wa majinyaci numfashi, duk ita kadai.

A Alhamis din nan jihar New Jersey ta ba da rahoton cewa adadin mutanen da aka sani sun kamu da cutar covid19 ya k'aru da kusan mutum 2,500 cikin kwana guda. Haka ma adadin mutanen da suka mutu a jihar ya kai 81.

Shi ma wani likitan kai daukin gaggawa kuma mai koyarwa a kwalejin koyon aikin likitanci ta Harvard da ke Boston, Dr Jeremy Samuel Faust, ya fada BBC cewa karfin barkewar wannan annoba a Amurka ya nuna cewa, cutar ta shammaci kasar.

"Lamarin na nuna cewa mun gaza shawo kan bazuwar wannan kwayar cuta. Akwai ji-ji da kan cewa wannan abu ba zai iya faru a kanmu ba, wannan matsalar wasu ce. Mun rika jin cewa muna da wata garkuwa da kariya ta daban. Ina jin mun samu kawunanmu da ma na shugabanninmu cikin mamaki."