Coronavirus a Najeriya: mutum 373 sun kamu da cutar ranar Alhamis

Covid-19

An gano sabbin mutane 373 da suka kamu da annobar korona a Najeriya ranar Alhamis - adadin masu fama da cutar ya kai 48,116.

A cewar alkaluman da hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a ƙasar ta fitar a shafinta na Twitter, cikin yini ɗaya an samu mutum 10 da suka mutu.

Adadin mutanen da suka mutu tun bayan da cutar ta ɓulla a Najeriya ya kai 966 sannan mutanen da suka warke kuma aka sallame su daga asibiti sun kai 34,309 jumulla.

Cikin yini ɗayan, Legas, inda annobar ta fara ɓulla a ƙasar ta na da mutum 69 da suka kamu da cutar kuma ya zuwa yanzu, jihar na da mutum 16,256 da ke fama da annobar.

Osun kuma ta na da mutum 41 da cutar ta harba ranar Alhamis sai Kaduna da Oyo da mutum 40 suka kamu a kowace jiha.

Abuja, babban birnin Najeriya da take ta biyu a jadawalin inda aka fi samun masu fama da cutar ta na da mutum 35 da a cikin sa'a 24 suka kamu da cutar.

A jihar Plateau kuma, an samu mutum 22 da suka kamu da cutar cikin yini ɗaya kuma a jihar baki ɗaya mutane 1,665 ne suke fama da annobar.

A Rivers mutum 19 ne suka kamu sai Kano da Ondo da ake da mutum 17 a kowace jiha. Ita kuma Ogun an samu mutum 15 da suka kamu da annobar.

Abia ta samu mutum 14 da suka harbu da korona - jihar na da mutane 677 da suke da cutar kenan.

Gombe na da mutum 12, sai Imo mai mutane 9 yayin da Enugu aka samu mutum 7 da suka kamu da korona cikin sa'a 24 da suka gabata.

Sai Kwara mai mutane 6, Delta na da 5 sannan Neja na da biyu. Borno da Bauchi da Nassarawa suna da mutum ɗaya kowace jiha.

Muhimman bayanai kan annobar korona

Ranar Laraba 16 ga watan Yuni ne Najeriya ta ba da rahoton mutuwar mutum 31 sakamakon cutar ta korona, shi ne adadi mafi yawa na mace-macen da aka samu cikin sa'a 24 a ƙasar.

Sai kuma Laraba 1 ga watan Yuli, inda aka samu adadi mafi yawa zuwa yanzu na mutum 790 da suka kamu da cutar.

An fara gano ƙwayar cutar korona a Najeriya ne a jikin wani baturen kasar Italiya ranar 27 ga watan Fabrairu bayan ya shiga kasar ta filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas.

Shi da mutum na farko da ya kamu da cutar ranar 20 ga watan Maris a arewacin Najeriya, Mohammed Atiku duk sun warke kuma an sallame su daga asibiti.

A ranar Juma'a 17 ga watan Afrilu ne cutar korona ta yi sanadin mutuwar Malam Abba Kyari, shugaban ma'aikatan fadar shugaban Najeriya. Shi ne mutum mafi girman mukami da ya mutu dalilin korona a kasar.

Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta da ke kudu maso kudancin Najeriya shi ne wani jagoran al'ummar jiha na baya-bayan nan da ya kamu da cutar korona ranar Laraba 1 ga watan Yuli.

Tun da farko gwamnoni irinsu Nasir El-Rufai na Kaduna da Bala Mohammed na Bauchi da Seyi Makinde na Oyo da Okezie Ikpeazu na Abia, da Rotimi Akeredolu na jihar Ondo duk sun kamu da annobar.

Hukumomin Najeriya dai sun ce sun rubanya yawan gwaje-gwajen da suke yi a kasar, inda a yanzu suka ce akan yi gwaji fiye da dubu ɗaya cikin sa'a 24.