Coronavirus: Yadda daukar hotunan taurari ya debe min kewa

Flame, Horse Head, Running Manm Orion, Messier 78 nebulas.

Asalin hoton, Dawid Glawdzin

Bayanan hoto,

An dauki hotunansa da na'urar kamara ta DSLR da kuma sandar kamara da ake kira tripod amma kuma ya ce mutum zai iya farawa da wayarsa ta salula mai daukar hoto da kyau

Wani mai masanin taurari kuma da ke daukar hoto ya ce kallon taurari ya taimaka masa sauyawa tare da jure wa kasancewa cikin yanayi na hana fita.

Dawid Glawdzin yana daukar hotuna daga lambunsa a Southend kusan shekara daya, yana tura wa shafukan Facebook.

Ya ce ya ga "ci gaba sosai" yadda mutane ke tambayarsa game da sha'awar aikinsa tun lokacin da aka kafa dokar ba da tazara domin yaki da coronavirus.

Yana daukar hotunansa da na'urar kamara ta DSLR da kuma sandar kamara da ake kira tripod amma kuma ya ce mutum zai iya farawa da wayarsa ta salula mai daukar hoto da kyau.

Asalin hoton, Dawid Glawdzin

Bayanan hoto,

Yana amfani da babbar na'urar kamara amma wani lokaci kamarar wayar salula na daukar hotuna masu kyau

Mr Glawdzin, mai shekara 37, ya dade yana sha'awar ilimin taurari da daukar hoto kuma ya yanke shawarar ya koyi yadda zai dauki hotunan samaniya.

"Za a ga gajimare da taurari a waje. Shi zai nuna komi da kuma ke nuna kankantarmu da rashin kima,"in ji shi.

"Maimakon daukar lokaci sauraren labarai da kafofin sadarwa na intanet, wanda zai iya zama damuwa. Na fi son na karkata zuwa ga abu mai amfani."

Asalin hoton, Dawid Glawdzin

Bayanan hoto,

Taurarruwar da ake kira Andromeda tana da kimanin haske shekaru miliyan 2 da rabi daga Duniya

Mr Glawdzin ye ce haske ne babban kalubalen da yake fuskanta wajen daukar hoto daga gida inda yake daukar lokaci yana kokarin sarrafa hotunan da kuma kokarin kaucewa hasken.

"Yawanci, ina daukar tsakanin 60 zuwa 200 na hotuna, daga nan na hade su zuwa hoto daya," in ji shi

Yana amfani da kamara mai kyau ta DSLR da ke juyawa kamar yadda duniya ke juyaya domin samun hoto mai kyau.

Ya jaddada cewa mutane na iya daukar hoton wata da kamara mai sauki ta DSLR ko kuma wayar salula ta zamani mai kyau.

Asalin hoton, Dawid Glawdzin

Bayanan hoto,

Dawid Glawdzin ya ce ya shafe shekara yana nazarin daukar hoton taurari

Asalin hoton, Dawid Glawdzin

Bayanan hoto,

Yana amfani da na'urar daukar hoto ta DSLR

Mr Glawdzin ya ce: "Mutane da dama na shigowa harakar kuma na lura akwai karuwar tambayoyin da ake tambayata.

"Ra'ayoyin da na samu sun kasance mai gamsarwa. Ya taimaka min wajen magance komai."

Asalin hoton, Dawid Glawdzin

Asalin hoton, Dawid Glawdzin

Dukkanin hotuna daga Dawid Glawdzin