Abin da ya sa Adam Zango ya yi rijista da hukumar fina-finan Kano

Bayanan sauti

Abin da ya sa na yi rigista da hukumar fina-finan Kano

Latsa alamar lasifika da ke hoton sama don sauraron hira da Adam A. Zango:

Tauraron fina-finan Kannywood Adam A. Zango ya ce ya yi rijista da hukumar tace fina-finai da dab'i ta jihar Kano ne domin kawo karshen matsalolin da abokan sana'arsa suke fada wa a cikin na rashin amincewa da fina-finansu.

Tauraron ya shaida wa Nasidi Adamu Yahaya cewa yin rijistar tasa zai ba shi damar zuwa Kano domin gudanar da sana'arsa ba tare da shamaki ba.

A cewarsa, "Na dawo na yi rijista da censorship board ne saboda dalilai biyu: na farko shi ne, furodusas dina da suke yin fina-finai da ni a jihar Kano a nan suka fi yawa.

''Sannan kuma yarana da nake tare da su da wadanda nake mu'amala da su dukka suna samun matsaloli wajen ba a kiran su ayyuka a dalilin wannan abu da ban yi ba. Wadansu ma sun yi rijista amma ba sa samun aiki saboda suna tare da ni."

Tauraron ya kara da cewa bai kamata son zuciya ya sanya shi ya zama silar hana wasu da ke kusa da shi samun aiki ba.

Sai dai ya kara da cewa har yanzu bai koma kungiyar Kannywood ba, yana mai cewa "ina nan a matsayin dan wasan fina-finai mai zaman kansa da ke Kaduna."

A watan Fabrairu ne hukumar tace fina-finai ta ce dole tauraron ya bi dokokinta idan yana so ya je jihar domin gudanar da harkokin fim.

Asalin hoton, Instagram/ADAM ZANGO

A wancan lokacin Adam A. Zango ya fito a wani bidiyo da tauraruwa Rahama Sadau ta wallafa a Instagram yana yi wa masoyansa Kanawa albishirin cewa zai je jihar domin kallon fim din 'Mati A Zazzau'.

Sai dai jim kadan bayan hakan ne wasu kafafen sadarwa na zamani suka ambato shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar, Isma'ila Na'abba Afakallah, yana shan alwashin kama tauraron idan ya sanya kafarsa a jihar.

Amma a tattaunawarsa da BBC, Afakallah ya ce ba su hana tauraron shiga jihar ba amma suna da dokoki game da zuwansa.

"Idan zuwa zai yi ya kalli fim kawai ya tafi shikenan, akwai wadanda ba su da rajista kuma suke zuwa su yi kallon su tafi babu ruwanmu da su.

"Kwanakin baya wannan hukumar ta yi kokarin tantancewa da tsafetace masu ruwa da tsaki a wannan harka kamar yadda doka ta ba ta dama."

Rayuwar Adam A Zano a takaice

  • An haife shi a garin Zangon Kataf a jihar Kaduna
  • Ya bar garin a 1992 bayan rikicin kabilancin da aka yi
  • Ya koma arayuwa a jihar Plateau inda ya yi karatun Firamare
  • Talauci ya hana shi cigaba da karatu a wancan lokacin
  • Tun yana yaro ake masa lakabi da Usher - mawakin nan dan Amurka saboda yadda yake rawa
  • Ya koma Kano inda ya fara aiki a wani kamfanin kade-kade da raye-raye
  • Fim dinsa na farko shi ne Sirfani, wanda ya ce shi ya shirya shi da kansa
  • Ya fito a fim sama da 100 a tsawon shekara 16

'Na fita daga Kannywood'

Tauraron fim din kuma mawaki ya ce daga yanzu zai fara cin gashin kansa ne, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Instagram.

Sai dai bai yi karin haske ba game da abin da yake nufi da fita daga kungiyar, ganin cewa akwai kungiyoyi da dama da suke cikin Kannywood.

Amma ya yi zargin cewa "ana yin shugabancin kama karya da rashin hukunta mai karfi ko arziki saboda kwadayi da son zuciya.

'Tuni na fara harkokina a Legas'

Kazalika, a watan Disamba dan wasan ya shaida wa jaridar Aminiya cewa shi fa ya koma jihar Legas da harkokinsa.

"Kamar dalibin ilimi ne da ya kammala karatun sakandare, idan yana so ya ci gaba da karatu sai ya tafi makarantar gaba da sakandare ko ya je jami'a, wannan ita ce manufata.

"Tuni na fara harkokina (a Legas), komai ya kankama. Ina shirin cikin wata shida zuwa shekara ɗaya zan dawo da iyalina gaba ɗaya nan Legas, har da mahaifiyata, cikin yardar Allah."

Karin labarai da za ku so karantawa: