Wane ne Dominic Raab?

Dominic Raab

Asalin hoton, EPA

Ofishin Firam Ministan Burtaniya, ya ce Boris Johnson ya bukaci Sakataren Harkokin Waje Dominic Raab ya taimaka masa "a bangarorin da suka dace", yayin da Mista Johnson din ke samun kulawa ta musamman bayan ya kamu da coronavirus.

Wane ne shi?

Kasa da shekara uku da ta wuce, Dominic Raab ba ya ma cikin gwamnati.

Amma yanzu, a matsayinsa na sakataren harkokin waje kuma mafi girma a sakatarorin gwamnati, shi ne kwatankwacin mataimakin Mista Johnson.

Wannan na nufin zai iya jan ragamar mulki na dan wani lokaci idan firai ministan ya ga rashin lafiyarsa ta ta'azzara.

Wannan wata dama ce da Mista Raab, tsohon lauya mai shekara 46, zai mora idan komai ya tafi dai-dai.

Mista Raab, mai tsananin kishin matakin ficewar Burtaniya daga tarayyar Turai, ya nemi shugabancin jam'iyyar Conservative a bara amma aka doke shi a zagaye na biyu inda 'yan majalisa suka kada kuri'a.

Kafin nan, ya sha kara wa da tsohuwar firai minista Theresa May, inda har ya ajiye mukaminsa a majalisarta bayan kwashe watanni hudu yana rike da mukamin Sakataren Ficewar Burtaniya daga Tarayyar Turai.

Mista Raab mai kaifin harshe, ya fuskanci sauye-sauye a siyasarsa - inda wani lokaci ya kan rasa madafa - tun da ya zama dan majalisa a jam'iyyar Conservative mai wakiltar Esher da Walton a gundumar Surrey tun shekarar 2010.

Wane ne Dominic Raab?

Asalin hoton, Getty Images

Ranar Haihuwa: 25 Fabrairu 1974 (shekarunsa 46)

Aiki: Sakataren harkokin waje kuma dan Majalisa a jam'iyyar Conservative mai wakiltar Esher da Walton

Ilimi: Makarantar Dakta Challoner's Grammar School da ke Amersham da jami'o'in Oxford da Cambridge

Iyali: Yana auren Erika Ray, wata 'yar asalin kasar Brazil kuma babbar jami'a a wani kamfanin kasuwanci. Yana da yara maza biyu

Kafin Siyasa: Lauya ne a Ma'aikatar Harkokin Waje. Shi ya jagoranci wata tawaga da ta mayar da hankali wajen tabbatar da an yankewa masu manyan laifuka hukunci a Babbar Kotun Duniya da ke The Hague

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

An haifi Mista Raab a shekarar 1974 kuma mahaifinsa wani Bayahude ne dan gudun hijira da aka haifa a kasar Czech wanda kuma ya tsere wa 'yan Nazi a shekarar 1938.

Ya girma a Buckinghamshire kuma ya yi karatu a makarantar Dakta Challoner's Grammar School a Amersham kafin ya tafi Jami'ar Oxford ya karanci aikin shari'a sannan daga baya ya koma jami'ar Cambridge inda ya yi digirinsa na biyu.

Ya yi aiki a matsayin lauya a bangaren kasuwanci da kuma Ma'aikatar Harkokin Waje kafin ya shiga siyasa a shekarar 2006 a matsayin mataimakin dan majalisa mai goyon bayan Brexit a jam'iyyar Conservative, David Davis sannan ya mai goyon bayan Dominic Grieve.

A shekarar 2010 aka fara zabarsa zuwa majalisar dokoki sannan a shekarar da ta biyo ta Mista raab ya bata wa Sakatariyar Harkokin Cikin Gida ta lokacin, Theresa May, bayan da ya bayyana wasu masu rajin kare hakkin mata a matsayin "masu son kai" a wata makala da ya rubuta a intanet.

Misis May ta zarge shi da rura wutar rikici tsakanin jinsin maza da mata.

Mista Raab ya kasance dan majalisar da bay a rike da ko wane mukamin gwamnati tsawon shekara biyar bayan da ya zama dan majalisar dokoki.

Amma kwararren dan damben Karate, Mista Raab ya zama karamin ministan shari'a bayan da David Cameron ya yi nasara a babban zabe a shekarar 2015.

Ya taka muhimmiyar rawa a kamfe din ficewar Burtaniya daga Taryyar Turai a zaben raba gardamar da Kungiyar Tarayyar Turai ta yi a 2016, amma Misis May ta sallame shi daga aiki lokacin da ta zama firai minister.

Matsayinsa a Majalisar Dokoki

A 2017, Shugaban Liberal Democrat na wannan lokaci, Tim Farron ya bayyana Mista Raab a matsayin mai "ban haushi" bayan da ya ce "mutumin da ke karbar sadakar abinci ba talaka ba ne illa kawai wanda bai iya tattalin kudinsa ba".

Amma a watan Yunin wannan shekarar ya koma gwamnati a matsayin matsakaicin ministan shari'a.

A lokacin da Misis May ta sauya ministocinta a watan Janairun 2018, ta mayar da shi ministan gidaje - daya daga cikin manyan ofisoshi a gwamnati.

Kuma a watan Yulin shekarar, lokacin da Mista Davis ya ajiye mukaminsa, firai minister ta kara wa Mista Raab matsayi zuwa sakataren Brexit, matsayi mai girma a cikin majalisar ministocinta.

Dangantaka mai kyau tsakaninsa da Misis May ba ta dade ba. A watan Nuwambar 2018, ya ajiye aiki inda ya soki matsayin da ta dauka kan Brexit.

A matsayinsa na mai fada a ji a batun Brexit, ana ganin muhimmancin kalamansa a kara karfin adawa ga yarjejeniyar Misis May ta ficewar Burtaniyar daga EU, wacce 'yan majalisar suka yi fatali da ita sau da dama.

Bayan da Misis may ta sanar da cewa za ta sauka daga mukaminta a bara, Mista Raab ya shiga takarar zama shugaban Conservative kuma firai minister.

A cikakkiyar majalisa, ya gaza samun kuri'u 33 daga 'yan majalisar da yake bukata ya kai zagaye na uku a zaben. Takwarorinsa masu goyon bayan Brexit Boris Johnson da Michael Gove sun doke shi.

Mark Francois, daya daga cikin 'yan majalisa masu tsananin goyon bayan Brexit y ace: "Duk wanda ya ci, kuma ina fata Boris ne, ina fata za su samu wani matsayi mai kyau su bai wa Dominic a majalisar ministocinsu, saboda ina ganin ya cancanci hakan."

Mista Johnson, wanda Mista Raab ya bai wa goyon baya bayan da aka cire shi a zagaye na biyu na takarar, ya dau shawarar da Francois ya ba shi. Ran 24 ga watan Yilin bara ya zama sakataren harkokin waje kuma babban sakatare - wato matsayin mataimakin firai minister kenan.

Asalin hoton, Reuters

Sabon mukamin ya ba shi girma a fadin duniya wanda matsayin Mista Johnson ne kawai ya wuce nasa, a gwamnatin Burtaniya.

Amma da kyar ya sha a babban zaben da aka yi a Disambar da ta wuce na matsayinsa na dan majalisar Esher da Walton inda abokin takararsa ya kalubalance shi da kuri'u 2, 743.

Nasarar da jam'iyyar Conservative ta yi, ta sa burinsa na ganin Burtaniya ta fice daga tarayyar Turai ya cika ran 31 ga watan Janairun wannan shekarar.

Tun bayan nan annobar coronavirus ta mamaye batutuwa a gwamnatin Burtaniya, duk da cewa tana ci gaba da tattaunawa kan yarjejeniyar kasuwanci da Taryyar Turan amma ta bidiyo ba a zahiri ba.

Yanzu Mista Raab, baya ga zama shugaban sakatarori, shi ne ke tafi da harkokin shugabancin kasar yayin da Mista Johnson ke samun kulawa a asibiti bayan da ya kamu da coronavirus.