Coronavirus: 'Yan sanda sun gargadi 'yan Najeriya kan 'yan damfara

IG MUHAMMAD ADAMU

Asalin hoton, NIGERIA POLICE FORCE

Wani batu da hukumomi ke gargadin 'yan Najeriya a wannan lokaci da ake zaman killace kai a gida shi ne hattara da 'yan damfara ta internet ko sakonnin waya.

Rundunar 'yan sandan kasar ta ja hankalin mutane da su yi hattara da sakonnin zamba da ta ce ana aike wa mutane domin karbar bayanan asusun ajiyar kudinsu na banki.

A wasu lokutan ma sakonnin na da alaka da bada tallafi ko kuma samun bayanai kan coronavirus.

Rundunar ta ce sashen gudanar da binciken laifuka na gudanar da bincike a kan irin wadannan matsaloli da aka shigar da su ofishinta.

Gwamnatin Najeriya ta hannun rundunar 'yan sanda a kasar, ta ce tana ci gaba da gudanar da binciken zamba cikin aminci wadanda ' yan kasar suka gabatar a ofishin 'yan sanda.

Babban jami'in hulda da jama'a na 'yan sanda a Legas DSP el-Kana, ya ce tun da aka kafa dokar takaita zirga-zirga 'yan damfara suka shiga laluben sabbin hanyoyin yaudarar mutane.

El-Kana ya ce '' Migayun kan aike sakonni a wayoyin mutane sai su shaida musu cewa su jami'an gwamnati ne da ke rabon tallafi, hakan na basu damar karban bayanan mutane na Banki''.

''A wasu lokutan kuma sukan fake da jami'an kamfanonin sadarwar - Glo ko MTN ko Airtel - sai su bukaci ka aike wasu sakonni wanda hakan ke basu damar kutsawa wayarka da satar bayanai.''

DSP El-kana, ya gargadi 'yan kasar da su yi hatttara da irin wadannan sakonni kuma su nesanta kansu da aike sako ko bada bayanansa.

'' Muna aiki tare da jami'an bankunan don haka duk wanda ya samu irin wannan sako ya tuntubi 'yan sanda domin su tuntubi jami'an banki don tabbatar da sahihancin sako''.

Tun bayan bular coronavirus a kasar ana ta samun rahotanni yada labaran bogi ko tura sakonni a waya kan wannan cuta.

Wannan ba shi ne karon farko da ake jan hankulan al'umma da su guji irin wadannan labarai ko sakonni ba.

Sai dai a wannan lokaci mahukunta a kasar sun ce sun dukufa domin dakile ko yakar irin wadannan mutanen ta hanyar neman hadin kan duk wanda ya karbi irin wannan sako na damfara.

Karin labaran da za ku so ku karanta