Coronavirus: Yadda mata za su kare kansu daga cutar

Kwayar cutar covid-19

Asalin hoton, Getty Images

Kwararru a fannin lafiya sun dukufa wajen fadakar da mata a kan yadda za su kiyaye da tsaftar jikinsu domin kaucewa kamuwa da cutar Coronavirus.

Kwararrun sun ce akwai abubuwan da yakamata mata su rinka kula da shi a wannan yanayi da ake ciki na annobar covid-19.

Dakta Maryam Mustapha, ta shaida wa BBC cewa babban abin da ya kamata matan su yi shi ne daukan matakan kariya saboda mata su ne masu kula da gida kama daga kan maigida da yara da ma su kansu.

Ta ce babban abu mai muhimmanci wajen kariya shi ne a rinka yawan wanke hannaye akai-akai kamar yadda hukumar lafiya ta duniya ta bayyana.

Dakta Maryam ta ce "Abin da yakamata mu sani shi ne ita fa wannan cuta yaduwa take, don haka sai mata su kula da hanyoyin da cutar ke bi wajen yaduwa sai a kare kai".

Ta ce, hanyoyin sun hadar da idan ka hadu da wanda ke dauke da cutar idan yana tari ko atishawa sai a bayar da tazara kamar ta mita daya.

Likitar ta ce, kwayoyin wannan cuta su kan sauka a wurare daban-daban, kamar inda mutum zai dora hannunsa ko kuma inda ake dora kaya, to dole ne a kula.

Ta ce " Yakamata mata su guji shiga cikin mutane domin yanzu ba lokaci bane na ziyara ko zuwa gidan biki.

Dakta Maryam ta ce, ya kamata matan su rinka sanya takunkumin fuska musamman idan za su fita saboda su kare kansu.

Likitar ta ce, idan kuwa maigida ne ya fita unguwa, to da zarar ya dawo a kai masa ruwa da sabulun wankin hannu ya wanke hannunsa kafin ya taba komai a gidan hatta yara.

''A wasu lokutan idan maigida zai fita to idan da hali sai a bashi man tsaftace hannu wato hand sanitizer a turance kenan, ace masa ya shafa saboda gudun kada ya kwaso wa iyali jangwam.''