Chelsea za ta dauko Coutinho, Man Utd da Napoli na zawarcin Rodriguez

Philippe Coutinho

Chelsea tana tattaunawa da zummar sayo dan wasan Barcelona da Brazil Philippe Coutinho. Yanzu haka tsohon dan wasan na Liverpool mai shekara 27 yana zaman aro a Bayern Munich. (Sport)

Manchester United da Napoli suna son sayo dan wasan Real Madrid dan kasar Colombia James Rodriguez, mai shekara 28. (AS, in Spanish)

Dan wasan Aston Villa dan kasar Ingila Jack Grealish, mai shekara 24, na cikin manyan 'yan wasan da Manchester United take son daukowa idan aka bude kasuwar musayar 'yan kwallon kafa. (Evening Standard)

Barcelona ta barar da damar sayo dan wasan Chelsea da Brazil Willian, duk da yake a karshen kakar wasan bana za a bar dan wasan mai shekara 31 ya sauya kungiya. (Sport)

Amma Chelsea ta soma tattaunawa da dan wasan baya Antonio Rudiger. Kungiyar tana son dan wasan na Jamus mai shekara 27, ya sanya hannu a sabuwar kwangila wacce za ta tsawaita zamansa zuwa 2023. (Sky Sports)

Napoli na zawarcin dan wasan West Ham dan kasar Brazil Felipe Anderson, mai shekara 26. (Corriere dello Sport, in Italian)

Besiktas na duba yiwuwar sayo golanBurnley Joe Hart, mai shekara 32, domin maye gurbin golan Jamus mai shekara 26 Karius, wanda yake zaman aro a Liverpool.(Fanatik, in Turkish)

Brighton na dab da kammala sayen dan wasan Sydney FC da ke buga kasar Under-17 a Australia Cameron Peupiona, mai shekara 17. (Sydney Morning Herald)

Dan wasan baya Diego Carlos ya ce yana cike da farin ciki a Sevilla duk da zawarcinsa da Liverpool take yi. Za a sayar da dan wasan mai shekara 27 dan kasar Brazil a kan £64m. (Estadio Deportivo, in Spanish)

Dan wasan Liverpool da Senegal Sadio Mane, mai shekara 27, ya ce ya duba yiwuwar komawa Manchester United kafin ya koma Anfield.