An kama shugaban ma'aikatan shugaban Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo

Jam'iyyar Mr Kamerhe (Hagu) ta goyi bayan Mr Tshisekedi a zaben shugaban kasar da aka gudanar a 2018.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Jam'iyyar Mr Kamerhe (Hagu) ta goyi bayan Mr Tshisekedi a zaben shugaban kasar da aka gudanar a 2018.

An kama shugaban ma'aikatan fadar shugaban Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo ranar Laraba a Kinshasa, babban birnin kasar awowi da dama bayan an yi masa tambayoyi kan zargin kashe kudi ba bisa ka'ida ba.

An yi wa Vital Kamerhe tambayoyi kan rawar da ya taka game da zarge-zargen cin hanci a kwangilar gudanar da manyan ayyuka wadda ke karkashin kulawarsa a kwanaki 100 na wa'adin da ya wuce na jagorancin Shugaba Félix Tshisekedi's a bara.

An yi awon gaba da shi zuwa babban gidan yarin kasar mai suna Makala, inda ya kwashe daren jiya.

Ba a sani ba ko za a tuhume shi a kan zarge-zargen.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambato mai magana da yawun Shugaba Tshisekedi yana cewa "shugaban kasa ba ya tsoma baki a kan harkokin da suka shafi shari'a".

Magoya bayan Mr Kamerhe sun yi zanga-zanga a mahaifarsa da ke Bukavu, a gabashin Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo sannan suka toshe hanyar shiga hedikwatar jam'iyyarsa, a cewar AFP.

Jam'iyyar Mr Kamerhe ta Union for the Congolese Nation (UNC) ta goyi bayan Mr Tshisekedi a zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Disambar 2018.