Coronavirus: Ina annobar ta kai a arewacin Najeriya?

Abba Kyari

Asalin hoton, Facebook/Buhari Sallau

Baya ga Abuja, babban birnin tarayya, jihohin Kaduna da Bauchi ne kan gaba a yawan masu fama da cutar coronavirus a yankin arewa, ko da yake, Katsina wadda aka fara sanar da bullar annobar ranar Talata 7 ga wata, tana kokarin kamo su.

Yanzu dai akwai mutum biyar da aka tabbatar sun kamu, bayan sake samun mutum 1 mai fama da cutar a ranar Lahadi.

Gwamnatin jihar Katsina dai ta shelanta kulle Daura, mahaifar shugaban kasar, inda aka samu mutum na farko da ya kamu da cutar.

Sai dai babu jimawa kuma sai aka ji annobar ta bulla karon farko cikin Kano, jiha mafi yawan jama'a a Najeriya kuma cibiyar hada-hadar kasuwanci don haka ne ma ake da damuwa sosai game da al'amarinta.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce yana duba yiwuwar rufe wasu kasuwanni kuma zai yi ganawa da malaman Kano don sanin yadda za su bullowa lamarin taruka irin na Sallar Juma'a da haduwar ibada a coci-coci.

Asalin hoton, @dawisu

Bayanan hoto,

Tuni dai gwamnatin jihar ta sanar da rufe kan iyakokin shiga Kano

Jimillar mutanen da suka kamu da cutar koronabairas a daukacin yankin sun kai 80 zuwa ranar Lahadi, a cewar hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Najeriya.

Abuja ce ke da mafi yawam mutanen da ke fama da annobar a yankin, an fara samun bullar wannan cuta a babban birnin ranar 20 ga watan Maris, bayan gwajin da aka yi wa Mohammed Atiku.

Ga alama har yanzu d'an na Atiku Abubakar, jigon dan siyasa a Najeriya yana ci gaba da jinya a cibiyar kebe marasa lafiya ta Gwagwalada a Abuja.

Wasu sun rika yaba wa jarumtarsa ta fitowa ya yi wannan bayani, wasu kuma sun rika zargin dan Atikun da rashin kebe kansa bayan ya dawo daga wata tafiya kasashen waje.

Asalin hoton, Facebook

Bayanan hoto,

Engineer Sulaiman ya yi fama da cutar daji da ciwon suga kafin annobar Coronavirus ta kama shi

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

A ranar Litinin 23 ga watan Maris ne Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta ba da sanarwar samun mutum na farko da ya rasu sakamakon wannan annoba a Najeriya, lamarin da ya faru a Abuja.

Hukumar NCDC ta ce mutumin dan shekara 67 ya dawo gida Najeriya ne bayan ya je ganin likita kasar Burtaniya, a cewarta mamacin (Injinya Sulaiman A-ci-mugu) ya yi fama da wadansu kwantattun cutuka kafin rasuwarsa.

A ranar 7 ga watan Afrilu kuma, Gwamna Masari na jihar Katsina ya sanar cewa Allah Ya yi wa mutum na farko da ya kamu da coronavirus a jiharsa, Dr Aliyu Yakubu rasuwa.

Ya ce likitan wanda ke garin Daura, an ba da rahoton ya yi tafiya zuwa Lagos, kuma bai dade da komawa gida ba, sai ya kamu da rashin lafiya inda ya kai kansa asibitin rundunar sojan sama na Daura kafin cikawarsa.

Wasu na kuka wasu na dariya

Akasarin manyan mutanen da cutar ta harba da farko-farko sun fito ne daga jihohin arewa, inda a ranar Talata 24 ga watan Maris, hukumar NCDC ta sake fitar da bayanin cewa an samu mutum biyu da cutar ta harba a yankin, kuma karon farko cutar ta bulla a wata jiha, baya ga Abuja.

Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi shi ne jagoran wata jiha da covid-19 ta fara kamawa a Najeriya, ko da yake a yanzu ya warke har ma ya ci gaba da harkokinsa.

Asalin hoton, Facebook

Sai dai ya zuwa ranar Lahadi, akwai mutum biyar a jihar ta Bauchi da ke ci gaba da jinya sakamakon wannan annoba, ban da Gwamna Bala Mohammed da ya warke.

Haka shi ma, Mallam Abba Kyari shugaban ma'aikatan fadar shugaban Najeriya yana can yana ci gaba da jinya a jihar Legas, bayan an ba da rahoton kamuwarsa ranar 24 ga watan Maris.

Fitattun mutane irinsu Atiku Abubakar sun jajanta masa lokacin da rade-radin ya cika gari cewa annobar ta shafe shi bayan wata tafiya da ya yi zuwa kasar Jamus.

Asalin hoton, Facebook/Buhari Sallau

Haka kuma har yanzu babu wani rahoto da ke nuna cewa Malam Nasir El-Rufa'i, mutum na farko da ya kamu da cutar a jihar Kaduna ranar Asabar 28 ga watan Maris, ya samu sauki.

Yana cikin gwamnonin da suka fi zafafa daukar matakai don ganin annobar ba ta riski al'ummarsu ba.

El-Rufa'i dai ya dauki matakin kulle jiharsa ba shiga ba fita, tare da hana tarukan biki da na ibada ciki har da Sallar Juma'a da ibadu a coci-coci da masallatai.

Zuwa yanzu, akwai mutum shida da ke fama da cutar a jihar ta Kaduna, kuma daga bayanan hukumomi, ba a samu rasuwa sakamakon wannan annoba a jihar ba, kamar kuma yadda ba a samu wanda ya warke ba.

Mutum na baya-bayan nan da ya kamu da cutar, namiji da ke aikin gadi a unguwar Mando, bayanai sun ce an gano yana fama da corona ne bayan ya dawo daga tafiyar da ya yi zuwa jihar Legas, wadda ta fi yawan masu cutar a fadin Najeriya.

Binuwai ita ce jiha ta farko da wannan cuta ta fara bulla a yankin Arewa ta Tsakiya, inda hukumar NCDC ta ce zuwa ranar Asabar 28 ga watan Maris, adadin masu cutar a daukacin Najeriya ya kai 97.

Baya ga Binuwai cutar ta shiga jihar Kwara ranar 6 ga watan Afrilu, inda aka sanar da kamuwar mutum biyu.

Ran 09 ga watan Afrilu, an ba da sanarwar mutum na farko da annobar ta harba a cikin jihar Neja.

Tabawa ranar samu

Laraba 1 ga watan Afrilu a iya cewa tana cikin ranaku da aka fi samun mutanen da aka tabbatar sun sake kamuwa da annobar mafi yawa a arewacin Najeriya, inda adadin ya karu zuwa mutum 43.

Hukumar dakile cutuka ta ce an samu karin mutum bakwai da cutar ta shafa a Abuja, sai mutum 1 a jihar Kaduna da kuma karin wani a Bauchi.

Bayan sanar da kamuwar karin mutum uku a jihohin Kwara da Katsina a ranar Lahadi 12 ga Afrilu, adadin masu fama da cutar a daukacin yankin yanzu ya kai 80.

Nesa ta zo kusa

Sai dai wani karin ci gaba da aka samu a baya-bayan nan a yankin arewacin Najeriya shi ne bude sabbin cibiyoyin gwada cutar kovid-19.

Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta fada a ranar Asabar 11 ga wata cewa an yi nasarar bude cibiyoyin gwaji guda biyu a jihohin Kano da Filato.

Karon farko ke nan da aka samu irin wadannan cibiyoyin gwajin cutuka irinsu coronavirus a daukacin yankin arewa. Kafin yanzu sai dai a dauki samfur a kai shi zuwa Abuja ko Legas don tantancewa.

Asalin hoton, @NCDCgov

Hukumar ta kuma ce aiki na ci gaba da gudana don ganin an samu irin wadannan cibiyoyin gwaje-gwaje a biranen Maiduguri da Sokoto da kuma Kaduna.

Mutane nawa ne suka warke a arewa?

A ranar Alhamis, 9 ga wata, jami'an gwamnatin Bauchi, sun fitar da sanarwar cewa Gwamna Bala Mohammed ya warke har ma an sallame shi daga wurin da aka kebe shi.

Haka zalika, a ranar Lahadi 12 ga Afrilu, an ga bayanin da wani mashawarcin shugaban Najeriya kan harkar shafukan sada zumunta, Bashir Ahmad ya fitar da ke cewa an sallami karin mutum hudu bayan warkewarsu daga cibiyar Gwagwalada.

Duka-duka dai zuwa yanzu alkaluman hukumar NCDC na cewa mutum 85 ne suka warke a daukacin Najeriya.

Zuwa yanzu akwai tabbacin annobar ta bulla a jihohin da suka hadar da

Babban Birnin Tarayya - 56

Bauchi - 6

Kaduna - 6

Binuwai - 1

Kwara - 4

Katsina - 5

Neja - 1

Kano - 1