Kasashe masu arzikin man fetur za su rage man da suke fitarwa

Barkewar cutar Coronavirus a kasar Chana ya yi mummunan tasiri kan farashin man fetur a kasuwannin duniya
Bayanan hoto,

Barkewar cutar Coronavirus a kasar Chana ya yi mummunan tasiri kan farashin man fetur a kasuwannin duniya

An cimma wannan yarjejeniya ce yayin wani taro da kungiyar kasashe masu arzikin man fetur OPEC da Rasha da sauran kasashen da ke hako man fetur suka kira.

Bangarorin sun amince a zabge ganga miliyan 9 da dubu 700 da suke samarwa kullum, bayan shafe tsawon mako guda suna tattaunawa.

Da farko kasashen sun kuduri aniyar rage ganga miliyan goma ne a kullum, wanda ya kai kimanin kashi 10 cikin 100 na man da ake fitarwa kasuwannin duniya, sai dai Mexico ta sa kafa ta shure adadin da aka nemi ta rage.

Kasashen masu arzikin man fetur za su fara rage man da suke hakowa ne daga ranar 1 ga watan gobe, kuma yarjejeniyar za ta kai har karshen watan Yuni, daga nan kuma za a fara sassauta matakin sannu a hankali har zuwa shekara ta 2022.

Tun a farkon watan jiya ne, farashin man fetur ya yi faduwar da bai taba yin irinta ba kusan a cikin shekara ashirin.

Haka zalika, bukatun man fetur din sun yi matukar raguwa sakamakon annobar coronabairas, abin da ya kara ta'azzara lamarin.

Wani kwararre kan harkar makamashi, Sandy Fielden, ya fada wa BBC cewa yarjejeniyar ba a taba ganin irinta ba saboda ba kawai a tsakanin kungiyar OPEC ba ne da Rasha har ma da kasar da ta fi samar da man fetur a duniya wata Amurka da kuma sauran kasashen kungiyar G-20.

Ya ce yarjejeniyar tana da matukar muhimmanci don kuwa: "Komai ya dogara ne a kan makamashi.

A yanzu, tabbas babbar matsalar da ta fi damun harkokin man fetur ita ce ba ma amfani da makamashi mai yawa saboda an rufe kasashe ba shiga ba fita.

Man fetur da ababen sufuri ke sha ya yi matukar raguwa da kimanin kashi daya cikin uku."

Shugaba Donald Trump dai ya bayyana lamarin a matsayin wata gagarumar yarjejeniya. A 'yan kwanakin nan ya yi ta matsa wa Mexico lamba, wadda ta ki amincewa ta rage nata kaso.