Yau shekara 13 da kisan Sheikh Jafar a Kano

Sheikh Jafar Mahmud

Asalin hoton, Twitter/Sheikh Jafar Mahmud

Bayanan hoto,

An haifi marigayin ne ranar 13 ga watan Fabrairun shekarar 1961 a Daura

A ranar Litinin ne fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na Najeriya, Sheikh Jafar Mahmud Adam ya cika shekara 13 da rasuwa.

Wadansu 'yan bindiga ne suka harbe malamin yayin da yake Sallar Asuba a ranar 13 ga watan Afrilun shekarar 2007 a Kano - wato a jajiberin zaben gwamnoni wanda aka yi a shekarar.

Marigayin yana daya daga cikin manyan malaman addini a bangaren mabiya Sunnah da ke da dimbin magoya baya.

Kuma bayan wallafa hotonsa a shafukanmu na sada zumunta a ranar da ya cika shekara 13 da rasuwa mun samu dubban sakonnin da nuna alhini game da mutuwarsa.

Duk da cewa har yanzu jama'a na ci gaba da bayyana mutuwarsa a matsayin wani babban rashi, amma kuma har yanzu babu wani da aka kama laifin kisan malamin.

Sai dai a wani bidiyo da shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya fitar a watan Fabrairun 2020 ya yi nuni da cewa su ne suka kashe malamin.

Wane ne Sheikh Jafar Adam?

  • An haife shi ne a ranar 12 ga watan Fabrairun shekarar 1961 a Daura jihar Katsina
  • Ya koma Kano don yin karatun allo yana da kimanin shekara hudu a duniya
  • Ya fara yin karatun addini ne a wurin mijin yayarsa
  • Ya haddace Al-Kur'ani a shekarar 1978
  • Ya fara karatun boko ne a shekarar 1990
  • Ya yi karatun addinin Musulunci a kasashen Saudiyya da Sudan, inda ya samu digiri na biyu.
  • Yana koma wa garin Maiduguri duk shekara don gudanar da tafsirin Al-Kur'ani a kowane watan azumin Ramadan

Ga yadda jama'a suka rika bayyana alhininsu game da zagayowar ranar rasuwar malamin a shafinmu na Facebook kamar haka.

Tunatarwa: Mun soma wallafa wannan labarin ranar 13 ga watan Afrilun 2019, yanzu kuma muka sabunta shi.