Coronavirus: Likitocin China sun tafi Afirka don bayar da agaji

Likitocin da su je Habasha da Burkina Faso don yak ida cutar korona
Bayanan hoto,

Likitocin da su je Habasha da Burkina Faso don yak ida cutar korona

Tawagar likitocin China ta tafi kasashen Habasha da Burkina Faso domin bayar da tallafi a kokarin yaki da cutar korona, a cewar gidan talbijin na China Global Television Network.

Ba a bayyana adadinsu ba, amma sun fito ne daga lardunan Sichuan da Tianjin Municipality.

Ma'aikatar harkokin wajen China ta ce sun bar kasar zuwa Afirka ne ranar Alhamis.

An ambato kakakin ma'aikatar wajen China Zhao Lijian yana cewa likitocin za su yi bayani kan yadda suka dakile cutar a kasarsu, sannan su bayar da koyar kan yadda kasashen biyu za su kawar da cutar korona.

Najeriya ma ta shigo da likitocin kasar China 18 domin su taimaka mata wajen yaki da cutar, ko da yake likitocin kasar sun bayyana rashin jin dadinsu.

Kungiyar likitoci ta kasar ta ce zai fi kyau a yi amfani da likitocin da ba su da ayyuka ko kuma wadanda aikin bai ishe su ba, domin yaki da cutar korona.

Rahotanni sun ce an kori daruruwan 'yan Afirka daga otal-otal dinsu a birnin Guangzhou domin gudun kada su yada wa mutane cutar korona.

Ministan harkokin wajen Najeriya ya bayyana rashin jin dadinsa kan matakin, inda ya ce a shirye kasarsa take ta kwashe 'ya'yanta daga China.

Karin labarai masu alaka: