Amurka na zargin Iran da tsokanar jiragenta a Tekun Fasha

Handout photo from US Navy showing Iranian Islamic Revolutionary Guard Corps Navy (IRGCN) vessels near US vessel in the Gulf (15 April 2020)

Asalin hoton, US Navy

Bayanan hoto,

Rundunar sojin ruwan Amurka ta ce a yayin da ake atisayen na ranar Laraba jiragen ruwan IRGC sun je daf da daf da jiragen ruwan Amurka suka kuma wuce su da gudu

Rundunar Sojin Ruwan Amurka ta zargi sojojin juyin juya halin Iran (IRGC) da ''yin wasu al'amura masu muni da tunzura'' a Tekun Fasha.

Jiragen ruwan sojojin Iran 11 ne suke ta ''tsokanar fadan'' wasu jiragen ruwan sojojin Amurka shida da jiragen Masu Tsaron Gabar Teku a ranar Laraba, a cewar Amurkan. Daya ma har ya wuce jirgin Masu Tsaron Gabar Teku da mita tara.

Jiragen sojin ruwan Amurka na wani atisayen soji ne da jiragen sojin Amurka masu saukar ungulu.

Har yanzu dai Iran ba ta ce komai ba.

Lamarin na zuwa ne kwana guda bayan da wasu mutane masu dauke da makamai da aka yi amannar jami'an IRGC ne - suka kwace ikon wani jirgin ruwan dakon mai na Hong Kong a Mashigin Tekun Fasha ta bangaren Oman, ta kuma karkatar da jirgin zuwa Tekun Fasha a bangaren Iran kafin daga baya su sake shi.

Rundunar sojin ruwan Amurka ta ce a yayin da ake atisayen na ranar Laraba jiragen ruwan IRGC sun je daf da daf da jiragen ruwan Amurka suka kuma wuce su da gudu ''wata alama ta takalar fada''.

Amurkan ta ce: "Matukan jiragen ruwan Amurkan sun sha aike gargadi ta hanyar sakon murya da kuma matsa oda, amma babu wata amsa daga IRGC din.

''Sai dai bayan kamar sa'a daya, jiragen ruwan IRGC sun mayar da amsar sakon murya, sai cikin dabara suka kauce daga kusa da jiragen ruwan Amurkan da ba da rata tsakaninsu.''

Rundunar sojin ruwan Amurka ta ce irin wannan ''ayyukan tsokana da tunzura suna kara barazanar yin taho mu gama,'' kuma ba sa cikin tsarin ayyukan teku na kasa da kasa.

A bara, dakarun Iran sun kwace jirgin dakon man Burtaniya a wani martani na kwace jirgin Iran din da aka yi a iyakar tekun burtaniya. Daga baya an saki dukkan jiragen dakon man.

Amurka ta kuma zargi Iran da kai hare-hare kan jiragen ruwanta shida a Mashigin Gulf na yankin Oman da kaddamar da hare-haren makamai masu linzami da jiragen yaki marasa matuka a wasu tasoshin man fetur na Saudiyya. Amma Iran ta musanta hannu cikin lamarin.

Tashin hankali tsakanin Amurka da Iran ya karu a watan Janairu, yayin da Amurka ta kashe babban janar na rundunar IRGC a wani harin sama a Iraki. Iran ta mayar da martani ta hanyar harba makamai masu linzami a sansanin sojin Iraki inda dakarun Amurka suke.