Jami'an tsaro sun yi kisa fiye da Coronavirus a Najeriya

IGP Mohammed Adamu

Asalin hoton, Facebook

Hukumar kare hakkin dan adam ta Najeriya ta ce jami'an tsaron kasar sun kashe akalla mutane goma sha takwas, yayin tilasta amfani da dokar hana zirga-zirga da aka kakaba a wasu jihohi don yaki da cutar korona.

Wannan adadi dai ya zarce na mutanen da cutar ta kashe a lasar baki daya, da ya tsaya a goma sha biyu.

Hukumar ta ce ta samu korafe-korafe fiye da 100 na take hakki, ciki kuwa har da wadanda tace sun shafi kisan jama'a.

A Najeriya dai hukumomi sun kakaba dokar hana zirga-zirga a manyan biranen kasar uku.

Ko da a ranar Laraba sai da wani likita ya mutu saboda kamuwa da cutar a birnin Legas.

Zuwa yanzu dai adadin mutanen da aka tabbatar suna dauke da cutar korona a Najeriya sun kai 407 kamar yadda hukumar da ke dakile cututtuka masu yaduwa a kasar NCDC ta sanar a ranar Laraba da daddare.

Tuni mutum 128 sun warke daga cutar yayin 12 kuma suka mutu.

Ya zuwa yanzu, cutar ta bulla a jihohi 19 har da babban birnin kasar.