Coronavirus: 'Girman barazanar da cutar take yi wa jihar Kano'

Bayanan sauti

Irin barazanar da cutar korona ke yi wa jihar Kano

Latsa alamar lasifika da ke sama domin sauraron Dr Nasiru Gwarzo a hirarsa da Buhari Muhammad Fagge

Likitoci da masana kiwon lafiya na ci gaba da tunatar da jama'ar jihar Kano kan matakan kariya da suka kamata su dauka domin kauce wa kamuwa da cutar korona.

Sun yi kiran ne bayan ma'aikatar Lafiya ta jihar Kano ta tabbatar da cewa ya zuwa karfe 11:55 na daren Laraba, an samu mutum 21 da aka tabbatar na dauke da cutar korona, inda mutum daya ya mutu sakamakon cutar.

Da daren Alhamis ne dai dokar hana zirga-zirga ta mako guda za ta fara aiki a jihar.

Dr Nasiru Sani Gwarzo, wani kwararren likita kuma dan asalin jihar Kano, ya yi kira ga 'yan jihar da su dauki matakan kariya kasancewar cutar za ta yi wa jihar barazana.

Dr Gwarzo ya ce dalilin da ya sa yake ganin akwai barazanar cutar korona a jihar ta Kano su ne:

  • Kwararar 'yan ci-rani daga Legas ko Abuja zuwa Kano
  • Mutanen Kano ba sa samar da tazara ko yin nesa-nesa da juna wajen mu'amala
  • Akwai mutane da dama da ke dauke da cutar ba tare da sun sani ba inda kuma suke yada ta
  • Rashin gwajin cutar ta korona

Dr Sani Gwarzo ya ce kasancewar kaso 80 cikin 100 na mutanen da cutar korona ke kamawa ba sa nuna wata alama inda suke warkewa ba tare da an yi musu magani ba, abin da ya sa likitan ya shawarci mutanen jihar ta Kano da su yi gwaji domin sanin hakikanin halin da suke ciki.

Har wa yau, masanin lafiyar ya ce ya kamata duk wani mutum da ya bar birnin Legas ko Abuja, to ya killace kansa na mako biyu kafin ya shiga cikin jama'a.

Bugu da kari, Dr Gwarzo ya ce wata hanya sahihiya ta yin rigakafi daga kamuwa da cutar ta korona, ita ce takaita shiga cunkoso da zama a gida.

Yanzu haka dai Kano ce ke biyewa birnin Abuja a yawan mutanen da cutar korona ta harba, inda Kanon ke da mutum 21 da suka harbu da cutar kamar yadda ma'aikatan Lafiyar jihar ta wallafa.

Rahotanni dai na nuna cewa 'yan ci-rani 'yan Arewacin kasar da ke zaune a jihar Legas na kwarara zuwa jihohin na Arewa kamar Kano tun bayan da aka saka dokar hana zirga-zirga a jihar ta Legas.

Tuni dai malamai a jihar ta Kano suka amince da dakatar da sallar Juma'a a daukacin masallatan jihar, a yayin da dokar hana fita da gwamnati ta saka ke fara aiki a yau Alhamis.