Coronavirus: Malamai sun amince da dakatar da sallar Juma'a a Kano

Asalin hoton, Getty Images
Malamai a jihar Kano da ke arewacin Najeriya sun amince da dakatar da sallar juma'a a daukacin masallatan jihar, a yayin da dokar hana fita da gwamnati ta saka ke fara aiki a yau Alhamis.
Malaman dai sun gudanar da taron nasu ne a Africa House da ke fadar gwamnatin Kano ranar Alhamis, karkashin kwamitin kar ta kwana na cutar korona da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kafa.
Idan an jima ne dokar hana fita da gwamnatin jihar ta kafa za ta fara aiki, wadda za a shafe tsawon mako guda.
Shawararin malaman dai na zuwa ne bayan da hukumomi a jihar Kano suka sanar da mutuwar wani mutum mai dauke da cutar korona a jihar, yayin da adadin wadanda suka kamu da cutar ya kai mutum 21.
Wakilinmu na Kano Khalifa Shehu Dokaji ya ce Malaman sun yi nazarin harkokin rayuwar al'umma ne wadanda ke da nasaba da taron jama'a da nufin bayar da fatawa, inda suka amince da dakatar da Sallar Juma'a a masallatan jihar da kuma tarukan da ake yi da suka shafi karatu a lokacin watan Ramadan, don hana yaduwar cutar korona a tsakanin al'umma.
Dr. Ibrahim Mu'azzam mai Bushira shi ne sakataren karamin kwamitin malamai da kwamitin kar ta kwana na coronavirus ya kafa, wanda ya ce malaman sun amince da a dakatar da gabatar da Sallar Juma'a don gudun kada wani da yake dauke da cutar ya yada ta a tsakanin al'umma.
Sai dai malaman sun ce dokar hana fitar za ta yi tasiri ne idan mahukunta da masu hannu da shuni suka agaza, kamar yadda Sheikh Mai Bushira ya ce.
Ganin yadda adadin masu kamuwa da cutar ke karuwa a Kano, da alama wannan matakin zai samu karbuwa ga dukkan bangarorin malamai a Kano, na dakatar da gabatar da Sallar Juma'a a masallatan jihar.
Jihar Kano dai na daga cikin jahohin da a baya-bayan nan aka sami bullar cutar korana a jihar, kuma alkaluman da mahukunta suka fitar sun nuna mutum 21 ne suka kamu da cutar zuwa yanzu, kuma daga ciki mutum guda ya riga mu gidan gaskiya a daren ranar Laraba.
Amma duk da ana kara samun masu dauke da wannan cuta a jihar, har yanzu ana ci gaba da cika sahun sallah a masallatai da dama, ba tare da an bayar da tazarar da jami'an lafiya ke ta kiran al'umma a kai ba.