Coronavirus: Likitoci na ba da wasiyya kan rashin tabbas

Ma'aikatan jinya na fuskantar barazanar kamuwa da coronavirus

A yayin da kasashen duniya ke ci gaba da yaki da annobar cutar korona ana iya cewa jami'an lafiya su suka fi shiga cikin barazana ganin cewa suke sahun gaba a fagen dagar dakile bazuwar annobar.

Likitoci da ma'aikatan jinya da na sa kai na cewa suna shiga cikin mawuyancin hali a asibitoci da kuma gidajensu bayan tashi aiki.

Dr. Hadiza Sulaiman Gachi, wata likita ce 'yar Najeriya da ke aiki a asibitin George Elliot da ke Birtaniya ta shaida wa BBC irin fargabar da yanayin da jami'an lafiya ke kwana da tashi a ciki.

Ta ce suna ganin marassa lafiya da dama wanda kullum karuwa suke cikin yanayin bukatar iskar da ke taimakawa numfashi, wasu kuma iskar ba ta isar su sai an dangana da basu kulawar gaggawa.

Likitar ta ce akasarin wadanda jikinsu ke tsanani maza ne da shekarunsu ke tsakanin 40 zuwa 60, 'yan shekaru 70 kuwa ba a cewa komai.

Dr Hadiza ta ce akwai fargaba sosai domin kullum tunaninsu shi ne suna iya kamuwa da cutar, kuma ta ya ya za su je gida cutar ba ta makale a jikinsu ko tufafi ba.

'' A kullum idan na tashi aiki ina cikin fargaba saboda muna kula da masu dauke da wannan cuta kuma za mu koma gida cikin iyali, ina tunanin ya zan shiga gida kar na yadawa diyata''

Bayanan sauti

Hira da Dr. Hadiza Sulaiman Gachi

Likitar ta ce suna kokarin ganin yadda za su rage kai cutar gida ta hanyar goge komai a cikin motarsu, kuma ba ta amincewa 'yarta ta taba ta sai ta yi wanka ta cire suturarta.

Ta ce ''Ya ta kullum tana cikin fargabar kar na kamu da cutar, kullum tsoro ne a fuskarta''.

Likitar ta ce iyalanta na tsorata sosai saboda ana yawaita maganar cewa basa samun isashshen kayayyakin kariya a yayin aikin kula da masu dauke da cutar korona.

Likitoci da dama na rubuta wasiyyar su saboda fargabar ba lallai su tsira daga wannan cutar ba, in ji Dr Hadiza.

Karin labaran da za ku so ku karanta