Saudiyya ta zartar da hukuncin kisa kan wanda ya kai hari gidan rawa

Mixed-gender concerts are now permitted in the kingdom

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A yanzu an dage haramcin cakuduwar maza da mata a wajen taruka a Saudiyya

An zartar da hukuncin kisa kan mutumin da ya daba wa a kalla wasu 'yan kasar Spaniya uku wuka a Saudiyya yayin da suke rawa a wajen wani taro.

An kai harin ne a wani dandalin casu da aka gudanar a Riyadh don nishadi, a watan Nuwamba.

Majiyoyin kasar sun alakanta maharin mai suna Imad al-Mansouri dan kasar Yemen mai shekara 33 da kungiyar Al-Qaeda,

Lamarin ya faru ne a yayin da Saudiyya ta sassauta tsauraran dokokinta kan nishadi.

Harin ya faru ne ranar 11 ga watan Nuwamba yayin da wani mutum ya durfafi Dandalin Sarki Abdullah da ke R|iyadh ya daba wa masu rawa a wajen wuka.

Wata kotu ta musamman da ke yin hukunci kan abin da ya shafi ta'addanci ta samu al-Mansouri da laifuka da dama da suka hada da bin umarnin wani babban dan al-Qaed a Yemen.

An kashe shi ne a birnin Riyadh a ranar Alhamis, kamar yadda ma'aikatar harkokin cikin gida ta fada a wata sanarwa.

Kungiyar Al-Qaeda ba ta ce ta ita ta kai harin ba.

Daya mutumin da suka aikata laifin tare kuma an yanke masa hukuncin daurin shekara 12 da rabi a gidan yari.

Hukumomin Saudiyya sun yi ikirarin cewa al-Mansouri ya dauki bidiyon kansa yana sukar sabuwar Hukumar Kula da Bangaren Niahsadantarwa ta kasar, kuma bidiyon ya yadu a shafukan sada zumunta.

Yarima mai jiran gado Mohammed Bin Salman ya yi alkawarin kawo sauye-sauyen zamani da ake kira Vision 2030, tun bayan nadinsa a shekarar 2017.

Sauye-sauyen sun hada da bude gidajen sinima tare da kashe kudade wajen hada casu ga manyan mawaka da shirya damben zamani na maza da mata da kuma bai wa mata izinin tukin mota.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wani taron kalan-kuwa da aka yi a watan Disamba a Riyadh shi ne mafi girma da aka taba yi a kasar

Hukumomin Saudiyya sun ce suna son samar da kudin shiga dala biliyan 64 daga bangaren nishadi daga cikin matakan rage dogaro da arzikin fetur.

Shekarun baya dai wani ba zai taba mafarkin za a gudanar da irin wannan casu ba a Saudiyya, amma yarima mai jiran gado Mohammad Bin Salman ya kawo sabbin sauye-sauye.

Hukumomin Saudiyya sun ce harin na watan Nuwamba shi ne na farko tun bayn sanar da sauye-sauyen