Coronavirus: Yadda za ku kare kanku, da hana yaduwarta da bin shawarwarin WHO

An fara wallafawa ranar 21 ga watan Afilun 2020

Sneezing a tissue and disposing of it immediately is one of the basic measures to protect against Covid-19

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Idan kuka yi atishawa ko tari, ku rufe hancinku da tolifefa ko kuma idan ba ku da ita, ku lankwasa gwiwar hannunku, ku yi atishawar ko tarin a ciki

Cutar korona ta zo da sauye-sauye da dama game da yadda muke rayuwa da yadda muke mu'amala.

Amma yawan shawrawarin da ake bayarwa kan yadda za mu kare kanmu da wasu a lokacin annobar na iya yi mana yawa.

Ga wasu abubuwa da za su taimaka maku.

Ya zan kare kaina?

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ku wanke hannuwanku a-kai-a-kai kuma sosai da ruwa da sabulu

A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, matakan kariya mafi muhimmanci kan cutar korona su ne tsafta.

 • Ku wanke hannuwanku a-kai-a-kai kuma sosai da ruwa da sabulu, ko kuma man wanke hannu mai sinadarin alcohol. Wannan na kasha kwayoyin cutar da ke kan hannuwanku.
 • Ku guji taba idanuwanku da hancinanku da bakunanku. Kuna taba wurare da yawa da hannuwanku kuma suna iya kwasar kwayoyin cuta. Daga nan, kwayoyin cutar na iya shiga jikinka idan ka taba shi da hannuwan naka.

Yaya za mu hana yada cutar?

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ku jefa tolifefar da zarar kun gama amfani da ita

 • Idan kuka yi atishawa ko tari, ku rufe hancinku da tolifefa ko kuma idan ba ku da ita, ku lankwasa gwiwar hannunku, ku yi atishawar ko tarin a ciki.
 • Ku jefa tolifefar da zarar kun gama amfani da ita. Wannan zai hana kwayoyin cutar da ke jiki isa ga sauran mutane.
 • Haka kuma, ana ce wa mutane su rika barin tazarar a kalla mita 2 tsakanin juna - kwatankwacin tsawon hannun mutum sau biyu kenan.
 • A wurare da yawa, ana ce wa mutane su zauna a gida kuma kada su fita sai idan ya zama dole, don rage mu'amala da mutanen da ke tari da atishawa.
 • Idan kuka fita, Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ce yana da muhimmanci a guji yin musabiha, kuma a madadin haka ana iya daga hannu ko a rusuna kawai.

Shin takunkumi rufe fuska da safar hannu na aiki?

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Takunkumin rufe hanci da baki kamar wanda ake sayarwa a manyan kantuna ba zai kare ku daga kamuwa da cutar korona ba

Takunkumin rufe hanci da baki kamar wanda ake sayarwa a manyan kantuna ba zai kare ku daga kamuwa da cutar korona ba, saboda bas a rufe hancin da bakin soasai kuma bas a iya rufe idanuwa sannan ba a iya sa su tsawon lokaci.

Amma dai suna iya hana kwayoyin cutar da ke fitowa daga baki ko hancin marar lafiya su isa ga wasu.

Kada ku manta, mutane da yawa da ke dauke da cutar korona bas a nuna alamominta, don haka, babu laifi don an sa takunkumin rufe fuskar idan ana cikin mutane.

Safra hannu kuwa, WHO ta ce kuna iya kamuwa da cutar korona idan kuna amfani da su, kuma idan kuka taba fuskarku kwayar cutar na iya shiga jikinku.

A cewar WHO, yawan wanke hannu da ruwa da sabulu na ba da kariya daga cutar korona fiye da sa safar hannu.

Ya zan sani idan ina da cutar korona?

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Alomomin sun hada da tari mai zafi

Manyan alamomin cutar korona su ne zazzabi da tari marar fitar da majina - wadannan ne alamomin da ya kamata ku lura da su.

Ciwon wuya da ciwon kai da gudawa na daga cikin alamomin cutar a wasu lokutan kuma ana tunanin cewa wasu masu dauke da cutar na gaza jin kamshi da dandanon abinci.

Me zan yi idan na ji alamomin cutar?

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Idan kuka ji zazzabi da tari ko sarkewar numfashi, sai ku nemi shawarar likitoci don haka na iya nufin cutar ta yi tsanani

A cewar WHO, idan kuka ji alamomin ku zauna a gida, ko da kun ji ciwon kai da mura, har sai kun samu sauki.

Kada ku manta, a cikin kashi 80 cikin 100 na wadanda cutar ta kama, ba ta basu wahala sosai kuma yana da matukar muhimmanci ku guji mu'amala da sauran mutane.

Idan kuka ji zazzabi da tari ko sarkewar numfashi, sai ku nemi shawarar likitoci don haka na iya nufin cutar ta yi tsanani.

Ku buga wa hukumomin lafiya waya kafin ku je - saboda a halin yanzu asibitoci sun cika, amma suna iya gaya maku asibiti ko cibiyar lafiyar da za ku je.

Ya girman hadarin cutar Covid-19 yake?

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Amma idan ba a san yawan mutanen da suka kamu da cutar ba, babu yadda za a yi a gane yawan mutanen da Covid-19 ke kashewa

Sabon binciken da aka buga a mujallar kiwon lafiya ta The Lancet, ya yi kiyasin cewa kusan kashi 0.66 cikin dari na wadanda suka kamu da cutar za su mutu.

Wannan ya kere wa kashi 0.1 cikin dari na mutanen da mura mai zafi ke kashewa.

Amma idan ba a san yawan mutanen da suka kamu da cutar ba, babu yadda za a yi a gane yawan mutanen da Covid-19 ke kashewa.

Tattara yawan mutanen da suka mutu a lokacin annoba na da wahala, saboda akwai gibi a lokutan da mutane ke kamuwa da cutar da lokacin da take kashe su.

Alkaluman da aka fitar yanzu daga Kwalejin Imperial da ke Landan sun nuna cewa yawan mace-macen ya fi kan mutanen da shekarunsu suka haura 80 kusan sau 10, kuma mutanen da shekarunsu ba su wuce 40 ba, ba su cika mutuwa ba.

A binciken da aka yi kan mutane 44,000 daga China, mace-mace sun fi yawa a tsakankanin mutane masu fama da ciwon suga da hawan jinni da ciwon zuciya da cutukan numfashi, kusan sau goma.

Za a gano maganinta?

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Babu wasu magunguna ko riga-kafi na musamman da ake sha kan sabuwar cuta

Babu wasu magunguna ko riga-kafi na musamman da ake sha kan sabuwar cutar, kuma magungunan antibiotic bas a aiki a kanta (suna aiki a kan kwayoyin cutar bacteria amma bas a aiki kan virus).

Akwai magungunan da za a iya bayarwa, amma mutane da yawa na samun sauki ba tare da shan magani ba.

Masana kimiyya a fadin duniya na aiki tukuru don gani riga-kafinta, amma sai an yi gwaje-gwaje tukunna don haka ba kwanan nan za a fara amfani da shi ba.

Ta ya zan tabbatar da kwanciyar hankalina a lokacin wannan annoba?

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ku mayar da hankali kan abubuwan da ke faruwa yanzu kuma ku sawa ranku cewa annobar za ta zo ta wuce

Babu shakka, wannan lokaci ne mai rikitarwa.

Don haka, babu mamaki ku ji fargaba, tsoro, damuwa, bacin rai da gajiya.

Don taimaka maku a wannan lokacin annoba, Hukumar Lafiya ta Burtaniya ta samo wasu hanyoyin goma da za su iya taimaka maku:

 • Ku rika zumunci da 'yan uwa da abokan arzikinku ta hanyar buga waya ko shafukan sada zumunta
 • Ku bayyana masu abubuwan da ke damunku
 • Ku yi kokarin fahimtar damuwar da mutane ke ciki
 • Ku shirya wa sabuwar rayuwar da kuka tsinci kanku a ciki, kamar fita siyayyar kayan abinci da gudanar da ayyukanku na ofis daga gida.
 • Ku kula da jikinku ta hanyar motsa jiki a-kai-a-kai, ku ci abinci mai gina jiki sanna ku sha isasshen ruwa. Ku guji shan taba da yawan shan barasa
 • Ku bibiyi hanyoyin samun bayanai sahihai kuma ku takaita yawan bayanan da kuke karantawa ko kallo dangane da annobar
 • Ku rungumi mawuyacin halin da kuka tsinci kanku a ciki: ba wani abu ba ne don kun amince abubuwa sun tabarbare, amma kuna iya mayar da hankali kan abubuwan da kuke iya sauyawa - kamar halayyarku
 • Ku yi abubuwan da ke kawo maku farin ciki.
 • Ku mayar da hankali kan abubuwan da ke faruwa yanzu kuma ku sawa ranku cewa annobar za ta zo ta wuce
 • Ku tabbata kuna samun isasshen bacci, kuma ku guji yawan shan abubuwa masu dauke da sinadarin caffeine sannan ku rage duba wayoyinku a lokacin kwanciya bacci.