Shin ko za a iya cewa yakin da ake yi da Boko Haram ya kusa zuwa karshe?

sojin Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

A 'yan kwanakin nan Najeriya ta yi ikrarin samun nasara a yakin da take yi da kungiyar Boko Haram, inda a wani yunkuri daya ta ce dakarunta sun kashe fiye da mayakan kungiyar 100.

Ko a watan Maris din da ya wuce kasar Chadi ta ce, ta kashe 'yan kungiyar fiye da 1,000.

Shin ko za a iya cewa yakin da ake yi da Boko Haram ya tasamma karewa idan aka yi la'akari da irin nasarori da Najeriya da makwabtanta ke ikirarin samu?

Masana na ganin idan har wannan nasara da wadannan kasashe ke ikirari gaskiya ce, to wannan ba karamin ci gaba ba ne da kuma gagarumar nasara da daukacin Yammacin Afrika.

To sai dai rashin samun wata kafar yada labarai mai zaman kanta da ke da damar tabbatar da wannan labari ya janyo dasa alamar tambaya game da wadannan jerin nasarori da rundunonin kasashen biyu ke ikirarin samu.

Masu sharhi na ganin akwai kamshin gaskiya game da wannan ikirari, an samu nasarar amma ba ta kai irin yadda kasashen ke ikirari ba.

Shugaban kasar Chadi Idriss Deby ya ce sojojin kasarsa sun kashe mayakan Boko Haram 1,000, da kuma hoton da yasa a shafinsa na Tiwita na gawarwakin mayakan da ba su fi 20 ba, ya janyo tambayoyi kamar haka; Ina sauran gawarwakin? A ina aka yi? Kuma da yaushe aka yi wannan ba-ta kashi?

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Malam Kabir Adamu shi ne shugaban Kamfanin Beacon Consulting da ke nazarin al'amuran tsaro a yankin Sahel, ya shaida wa BBC cewa "tana iya yuwuwa a samu galaba kan bangare daya a yaki amma hakan ba ya nufin an gama da shi yaki ya zo karshe.

Akwai abubuwa uku da za su iya tabbatar da wannan nasarar da ake ikirari, na farko a kama shugabannin wadannan kungiyoyi idan an ci galaba a kansu.

''Sannan a samu nasarar dakile hanyar da kudade da makamai suke shigarwa wadannan mayaka, sai na uku a dakile damar daukar sabbin mayakan da suke da ita a ko da yaushe."

Ya kara da cewa ''duka yakin da ake yi ana yin sa ne karkashin tutar rundunar yaki da Boko Haram ta kasa da kasa, ya kamata a samu cikakken hadin kai tsakanin kasashen biyu, amma akasin haka muke gani a ko da yaushe."

''Matukar ana son murkushe wadannan mayaka masu ikirari jihadi to sai an samu cikakken hadin kai tsakanin mambobin wannan kungiya,'' in ji Mallam Kabir.

Cikin fushi Shugaban kasar Chadi ya ba da sanarwar fitar kasarsa daga cikin gamayyar kasashen da ke wannan yaki a Tafkin Chadi, abin da ya janyo wani yunkurin rawar daji da Chadi ta kira ''Fushun Boma" wanda da shi ne ta ce ta kashe soji 1,000.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shugaban kasar Chadi Idris ya ba da sanarwar a kwanan baya cewa kasarsa ta janye daga gamayyar kasashen da ke yaki da Boko Haram a Tafkin Chad

Da an samu cikakken hadin kai tsakanin kasashen Kamaru da Nijar da Najeriya da Kuma Chadin, da wannan yunkuri watakila ya samu nasarar da ba a taba zato ba.

Abin da yasa ake maganar neman hujjar wannan nasara ta rundunonin nan shi ne, a baya gwamnatocin Najeriya sun yi ta ikirarin sun yi nasara a kan Boko Haram.

A 2015, an yi irin wannan gagarumin kokari na sojoji wanda ya sa shugaban kasar Muhammadu Buhari a watan 12 na shekarar ya fito ya yi ikirarin nasarar sojin Najeriya a kan ita Boko Haram, amma cikin 'yan shekaru sai aikinsu ya ci gaba yadda suka ga dama.

BBC ta yi makamanciyar irin wannan hirar da Barista Bulama Bukarti lauya mai zaman kansa a baya, inda yake cewa ''cikin shekaru biyar din da shugaban ya yi wannan ikirari duk shekara alkaluma na nuna mayakan Boko Haram na kashe mutum 2,000 a kasar.''

Ko a 2019, alkaluma sun nuna kungiyar ta kashe sojojin Najeriya da sauran jami'an tsaro 800.

Kafin wannan a 2017, sojojin Najeriya har tuta da Qur'ani suka kai wa Shugaba Buhari suka ce wannan ce alamar sun yi nasara a kan Boko Haram.

Amma a Disambar 2019, wannan kungiyar ta kai mummunan hari kan dakarun sojin Nijar, kuma a farkon shekarar nan suka kai hari kan sojin Chadi.

Karin labaran da za ku so ku karanta