Coronavirus a Nigeria: Gwamnonin arewa za su mayar da almajirai gidajensu

Almajirai a arewa

Asalin hoton, Getty Images

Gwamnonin jihohin arewacin Najeriya 19 sun sanar da rufe dukkanin makarantun tsangaya da zummar shawo kan annobar korona a yankin.

Akalla yara miliyan tara ne aka yi hasashen za a mayar da su gaban iyayensu sakamakon annobar.

Iyaye da yawa a arewacin Najeriya na tura yaransu zuwa makarantun allo domin samun karatun Al Kur'ani mai tsarki, wadanda suka hada da kananan yara 'yan kasa da shekara shida.

Ana bayyana damuwa kan makomar yaran, musamman yanzu da cutar korona ke ci gaba da bazuwa a jihohin arewancin Najeriya.

Wannan ne ya sa gwamnonin arewa suka yanke shawarar tura almajiran zuwa garuruwansu na asali daga cikin matakan da suke dauka na dakile bazuwar cutar a yankin.

Kuma tuni wasu rahotanni suka ce gwamnatin Kano ta tura almajirai da dama da suka fito daga jihar Katsina.

Baya ga daukar matakin haramta makarantun Almajiran, gwamnonin kuma a tattaunawar da suka yi sun bukaci gwamnatin Najeriya ta kara samar da wuraren gwaji a yankin - akalla cibiyar gwaji daya a dukkanin jihohin arewa 19.

Sun ce wannan zai kara taimakawa wajen gano masu dauke da cutar da kuma gaggawar magance ta.

An shafe makwanni babu cibiyar gwaji a yankin arewa duk da cutar na ci gaba da bazuwa a Najeriya, inda tafiyar hawaniyar da ake wasu ke bayyana fargabar cewa akwai mutane da dama da ke dauke da cutar da ba a gano ba.

Zuwa yanzu Najeriya ta tabbatar da mutum kusan 800 na dauke da cutar - kuma cutar ta fi yaduwa a kudancin kasar. Amma an samu karuwar yaduwar cutar a yankin arewa wanda ke kara haifar da fargaba a yankin.