Ramadan: Abubuwa 11 dangane da Watan Azumi

ramadan

Asalin hoton, Getty Images

A ranar Juma'a 24 ga watan Afrilun 2020 ne Musulman duniya suka fara azumin Watan Ramadan na shekarar 1441 bayan hijira.

A don haka ne BBC ta yi duba kan wasu abubuwa guda 11 masu muhimmanci da suka danganci wannan wata mai albarka.

1. Azumin watan Ramalana daya ne cikin rukunan Musulunci guda biyar.

2. A cikinsa ake samun daren Lailatul Qadri wanda falalarsa tafi na darare dubu, kimanin daren shekara 83 da wata hudu.

3. Tun daga farkon watan zuwa karshen ake bude kofofin Aljannah a rufe kofofin Wuta a sanya Shaidanu cikin dabaibayi.

4. Azumtar Watan Ramalana ke sanyawa a gafartawa Mutum abin da ya gabata na kura-kuransa.

5. A cikin Watan Ramalana a Daren Lailatul Qadr Allah ke saukar da bayanin abin da ya hukunta faruwarsa na shekarar bana zuwa shekara mai zuwa kamar yadda Al'qurani ya ambaci hakan a Suratul Qadri. (INNA ANZALNAHU FI LAILATIL QADRI)

6. Sadaka a watan Ramalana ta fi lada. An tambayi Annabi kan wace Sadaka ce ta fi? Sai ya ce: "Sadaka a Watan Ramalana".

7. A cikinsa Allah ya saukar da Alqur'ani dungurungum zuwa Baitul Izzah a sama ta farko, daga nan aka saukar wa Annabi Muhamamdu SAW a rarrabe.

8. Shi ne watan da in ka yi tsayuwar Sallah don neman lada a dararensa Allah ya gafarta maka abin da ya gabata na zunubanka kamar yadda Annabi ya ce.

9. A cikin kowane dare na Watan Ramalana ne Allah ke 'yanta bayinsa masu dumbin yawa daga cancantar zaman Wuta zuwa Aljannah.

10. Shi ne watan da yin aikin Umara a cikinsa yake daidai da Aikin Hajji da Manzon Allah kamar yadda Annabin ya fada a Hadisi.

11. A wannan Watan ne Annabi ya fi yawan kyauta kamar yadda Imamul Bukari ya ruwaito a Hadisi.

Bayanai daga Sheikh Dr Ibrahim Disina