Coronavirus: 'Yan sanda sun tarwatsa masu sallah a Kamaru

Wasu masallata

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kamaru na da masu dauke da cutar korona 1,430

'Yan sanda a Kamaru sun tarwatsa taron wasu Musulmai da suka je masallaci yin sallah.

Wannan arangama na zuwa ne a ranar farko ta watan Azumin Ramadana.

Masu ibadar sun bijire wa umarnin gwamnati ne na haramta taron mutane da yawa a wani mataki na shawo kan annobar korona.

Jami'an 'yan sandan sun tarwatsa masu ibadar ne daga masallatai 13 da ke yamma da tsakiya da kuma yankin arewa mai nisa na kasar.

A cewar wata sanarwa da rundunar 'yan sandan kasar ta fitar, masallatan sun sha alwashin cewa sai sun yi sallarsu.

Awah Fonka, shi ne gwamnan yankin arewa mai nisa, ya kuma shaida wa manema labarai cewa shi ne ya bai wa jami'an umarnin tarwatsa taron duk wasu masu ibada a cikin biranen Foumban da Foumbot da kuma Bafoussam da karfin tsiya.

Ya zuwa yanzu Kamaru na da masu dauke da cutar korona 1,430, yayin da 43 suka mutu saboda cutar.