Za a daina bulala a Saudiya - Kotun koli

Raif Badawi with children (family handout)
Bayanan hoto,

Hukuncin bulala da aka yanke wa Raid Badawi ya janyo ce-ce-kuce a duniya

Saudiya za ta soke bulala a ciki jerin hukunce-hukunce da ake yi wa mutane, kamar yadda wasu takardu da kafafan yadda labarai suka samu ke tabbatarwa.

Umarni da kotun kolin kasar ta bayar ya ce daga yanzu za a maye gurbin bulala da aike mutum gidan yari ko cin sa tara.

Kotun ya ce wannan na cikin sauye-sauye kan kare hakkin bil adama da Sarki Salman da dan sa ke bijiro da su, wato Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman.

Saudiya dai na yawan shan suka kan yadda take daure masu sukar tsarinta, da kuma kisan dan jaridar nan Jamal Khashoggi.

Masu fafutika sun ce Saudiya na cikin kasashen duniya da suka yi fice wajen tauye hakki, ana murde 'yancin fadin albarkacin baki da sukar gwamnati da hukunta mutane da suka soki manufofinta.

'Rage daraja'

A shekara ta 2015 hukuncin bulala da aka yi wa wani wanda ya yi fice wajen wallafa bayanai a internet, Raid Badawi ya ja hankali, an yanke masa hukunci ne bayan samun sa da aikata laifi ta internet da cin mutuncin addini.

An yanke masa hukunci bulala 1,000 a kowanne mako, sai dai kiraye-kirayen kasashen duniya da rahotanni da ke cewa ya kusa mutuwa sun sanya an dakatar da hukuncin.

Editan BBC kan harkokin kasashen labarawa Sebastian Usher ya ce wannan yanayi ya rage darajar kasar a idon duniya.

Da alama dai yanzu irin wannan hukuncin na neman zama tarihi a kasar.

Sai dai al'adar cafke masu nuna adawa da tsarin sarki da yariman kasar- ciki harda mata masu fafutika - na diga alamar tambaya kan kimar kasar, a cewar wakilin BBC.

Ko a wannan Juma'ar fitaccen mai fafutikar Saudiya ya mutu a gidan yari bayan shanyewar barin jikinsa, wanda masu rajin kare hakkin bil adama suka danganta da rashin samun kulawar mahukunta.