Mubarak Bala: Dalilin kama wanda ake zargi da cin zarafin Musulunci

Mubarak Bala

Asalin hoton, Mubarak Facebook

Bayanan hoto,

A shekarar 2014 ne Mubarak Bala ya ce ya bar Musulunci

Kungiyar kare hakki ta Amnesty International ta ce tana bibiyar halin da Mubarak Bala wanda aka ce shi ne shugaban wadanda babu ruwansu da addini a Najeriya yake ciki, bayan kamashi da jami'an 'yan sanda suka yi.

Amnesty ta ce ta damu matuka kan karuwar barazanar da ake yi wa rayuwarsa a kafafen sada zumunta a Najeriya.

A ranar Talata aka kama Mubarak Bala a jihar Kaduna, kuma ana sa ran za a mayar da shi Kano jiharsa ta haihuwa, inda a nan ne dimbin Musulamai suka rubuta wa hukumomi korafi da zarginsa da yin batanci ga Annabi Muhammad S.A.W.

'Yan sandan Kaduna sun kama Mubarak, wanda aka ce shi ne shugaban wadanda babu ruwansu da addini a Najeriya, bisa bukatar takwarorinsu na Kano. Ana zarginsa

Ana zargin ya ci zarafin addinin Musulunci ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Wata tawagar lauyoyi ce ta mika wa 'yan sanda korafi a Jihar Kano.

Tuni dai wasu masu rajin kare hakki suka yi ca a shafukansu na zumunta suna neman a saki Mubarak Bala, wadanda suka ce yana da 'yancin shiga addinin da ya kwanta masa a rai.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Barista Salisu Salisu Umar ne jagoran lauyoyin da suka yi korafi kan Mubarak, kuma ya fada wa BBC cewa ba don ya bar addinin Musulunci suka nemi a kama shi ba.

"Mun yi musu korafi ne kan aibata Annabi S.A.W. da ya yi a shafinsa na Facebook," a cewar Salisu Salisu.

Ya ci gaba da cewa: "Ba wai don ya yi ridda ba ne ko sabo, korafinmu a kan barin masu addini su yi addini ne."

"Abin da muke nufi shi ne, tun da shi (Mubarak Bala) ya bar Musulunci tun a shekarar 2014 bai kamata kuma ya rika aibata addinin ba da kuma abin da masu binsa suka yi imani da shi.

"A matsayinmu na lauyoyi, daga cikin hakkinmu mun nemi 'yan sanda su binciki abin da yake fada ko ya saba da abin da aka iyakancewa mutum ya yi magana kan addini."

Barista Salisu ya bayyana cewa suna so ne a hukunta shi da kundin tsarin mulkin Najeriya.

A shekarar 2014 ne matashi Mubarak Bala mai shekara 29, a lokacin, da ke birnin Kano ya ce bai yarda da samuwar Allah ba kuma ya ce ya bar addinin Musulunci.

Iyayensa sun kai shi asibitin masu tabin hankali domin binciken lafiyarsa a lokacin.

Karin wasu labarai da za ku so ku karanta: