Irrfan Khan: Tarihin marigayi Irrfan Khan, tauraron fina-finan Indiya

Irfan Khan

Asalin hoton, Getty Images

A ranar Talata da yamma 29 ga watan Afrilu ne Allah Ya yi wa fitaccen jarumin fina-finan Bollywood da Hollywood Irrfan Khan rasuwa bayan ya sha fama da cutar daji.

Jarumin mai shekara 53 a duniya ya rasu ne a wani asibiti da ke birnin Mumbai a Indiya.

Irrfan Khan na daya daga cikin kwararrun 'yan fim a Indiya kuma yana cikin manyan 'yan Bollywood da suka yi fice a fina-finan Hollywood.

Shaharraren dan wasan ya fito a fina-finai kusan 80, kuma a lokacin da yake cikin shekarunsa na 30 da 'yan kai, ya kusa barin harkar fina-finai bayan kwashe tsawon shekara 10 yana fitowa a fim amma bai yi fice ba.

Irrfan Khan ba shi da kamannin da aka fi so a taurarin fina-finan soyayya na Bollywood, amma ya yi fice a masana'antar da ma wasu fina-finan Hollywood kamar Life of Pi, Slumdog Millionaire da Jurassic World.

Khan ya kasance mutum mai zurfin tunani, kuma yana tofa albarkacin bakinsa kan batutuwa masu jawo ce-ce-ku-ce da suka danganci addininsa na Musulunci da masana'antar da ya yi wa aiki.

"Bana son Kalmar Bollywood," ya taba shaida wa Jaridar Guardian. "Wannan masana'antar na da nata salon wanda ba shi da alaka da Hollywood. Ta samo asali ne daga wasannin dandali na Parsi.

A gaskiya, taurari kalilan ne za su iya bugun kirji su ce sun kware a masana'antun biyu kamar Irrfan Khan.

Asalin hoton, CHUCK ZLOTNICK/NBCUNIVERSAL

Bayanan hoto,

Ya dage a kan zama dan wasan fim, duk da cewa 'yan uwansa da abokansa basu da burin haka a kansa

Rayuwarsa

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

An rada masa suna Sahabzada Irfan Ali Khan ran 7 ga watan Janairu a shekarar 1967 a kauyen Rajasthan da ke Tonk.

Dangin mahaifiyarsa sun fito ne daga gidan sarauta kuma mahaifinsa attajirin dan kasuwa ne mai sayar da taya.

Khan ya cire "Sahabzada" daga sunansa saboda yana bayyana cewa shi dan babban gida ne - ya yi tunanin wannan zai hana shi cimma burinsa.

Ya kuma sauya sunansa da "Irfan" zuwa "Irrfan" - ba don komai ba - sai don kawai ya fi son yadda sautinsa yake.

Da mahaifinsa ya rasu, ya bijire wa burin danginsa na cin gajiyar sana'ar sayar da taya. Ya dage a kan zama dan wasan fim, duk da cewa 'yan uwansa da abokansa ba su da burin haka a kansa.

"Babu wanda ya taba tunanin zan zama dan fim saboda ina da kunya, ga ni siriri. Amma burin da nake da shi ya tauye komai."

A 1984, ya nemi tallafin karatu a Makarantar Koyon wasan kwaikwayo ta kasa da ke Delhi.

"Na yi tunanin zan mutu idan ban samu shiga makarantar ba," ya shaida wa wani dan jarida.

A wannan makarantar ya hadu da matar da ya aura - marubuciya Sutapa Sikdar.

"Yana da mayar da hankali. Na tuna lokacin da yake dan makaranta idan ya dawo gida kai tsaye zai wuce dakin baccinsa, ya zauna a kasa ya kama karanta littafansa.

"Mu kuwa sauran sai mu zauna mu yi ta hira muna gulmace-gulmace," a cewarta.

Yin aikin da ba shi ya so ya yi ba

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

"Akwai lokacin da aka ki biya na saboda suna ganin ban iya fim ba gaba daya," kamar yadda ya taba fada

Ya nace zai yi aiki a masana'antar fina-finai amma ayyukan da ya rika samu daga farko-farko a kananan fina-finai ne. Shi kuma ba abin da yake so ba kenan.

Tsawon shekara 10, irin wadannan ayyukan ya yi ta yi musamman a tashoshin Zee da Star Plus. Ya yi tunani mai zurfi kan barin harkar fim kwata-kwata.

"Akwai lokacin da aka ki biya na saboda suna ganin ban iya fim ba gaba daya," a cewarsa.

Ya samu damar fitowa a wani babban fim wanda aka zaba cikin fina-finan da suka yi fice don ba da lambar girma ta Oscar mai suna Salaam Bombay!, amma ransa ya yi mugun baci da aka cire wuraren da ya fito a fim din a lokacin tacewa.

Wanda ya rubuta fim din ya tausaya masa amma ya gaya masa cewa "wani lokaci za ka yi nasara, wani lokaci za ka fadi".

Babban Fim

Ya yi fice bayan da ya fito a wani fim din Indiya da Burtaniya mai suna The warrior. An dauki fim din ne a Tsaunukan Himalayas da Hamadar Rajasthan.

Shi ne fim din farko da mai ba da umarni dan Burtaniya Asif Kapadia ya shirya. Ba shi da kudin biyan manyan taurarin Bollywood kuma yana neman fasihan 'yan wasa.

Irrfan Khan ya fito a matsayin wani gagarumin shugaban yaki.

Fim din ya ci lambar yabo ta Alexander Korda na fim din da ya fi kowanne a Bikin Karrama Fina-Finai na Burtaniya, BAFTAS.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

A shekarar 2008, ya hada kai da Danny Boyle suka shirya fim din 'Slumdog Millionaire

Nasarar da fim din 'The Warrior' ya samu ya zama silar shigar Irrfan harkar fina-finai ka'in da na'in, kuma shekaru 20 da suka biyo baya, ya tsinci kansa yana fitowa a fina-finai biyar zuwa shida a shekara.

Michael Winterbottom ya sa shi a fim dinsa na 'A Mighty Heart' a matsayin dan sanda da kasar Pakistan, kuma ya fito a fim din 'The Darjeeling Limited.'

A shekarar 2008, ya hada kai da Danny Boyle suka shirya fim din 'Slumdog Millionaire.' Khan ya fito a matsayin dan sanda da ke yi wa Dev Patel (Jamal) duka - saboda ya yi tunanin macuci ne.

Boyle ya bayyana kwarewarsa a matsayin "gwanin sha'awa".

Bayan nan, Khan ya kai matakin da sai ya zabi irin rawar da yake so ya taka a fina-finai.

"Ina kokarin yin fina-finan da za su yi tasiri mai dorewa, masu ma'ana, wadanda za ka so ka sake kallo bayan ka gansu a karon farko," ya shaida wa wani dan jarida.

Dangantakarsa da Musulunci

Asalin hoton, Ronald Grant

Ya kan ki yarda ya fito a fina-finan da suka danganci addini ko al'ada - ya ki amincewa ya taka rawa a fim din'Deepa Mehta'na Midnight's Children da fim din'Mira Nair' na Reluctant Fundamentalist.

Bayan harin 11 ga Satumba da aka kai a New York da Washington, sau biyu 'yan sanda na tsare shi a tashar jirgin sama ta Los Angeles saboda sunansa na kama da na daya daga cikin wadanda ake zargi da kai harin.

Ya yi kokarin cire sunan gidansu na Khan - inda ya fi so a rubuta masa Irrfan kawai ko a karshen fina-finan da ya fito.

Ya samu rashin jituwa da shugabannin Musulmi bayan da ya soki yin yanka da mabiya mazhabar Shi'a ke yi a watan Muharram.

"Muna yin wadannan abubuwan ba tare da sanin manufarsu ba," in ji shi.

Sun mayar masa da martani a fusace cewar ya mayar da hankali kan shirin fim kuma ya daina cewa komai kan addini.

A 2011, an ba shi lambar girma ta Padma Shri - lambar girma ta hudu mafi girma a Indiya, saboda gudumawar da ya bayar ga bangaren nishadi.

Bayan shekara guda, ya fito a fim din Life of Pi.

Kuma ya taka rawar kwararren masanin kimiyyar nan Rajit Ratha a fim din'The Amazing Spiderman'da Simon Masrani, attajirin nan mai gandun namun daji a fim din 'Jurassic World.'

Ya fito a fina-finan Blackmail da Puzzle na Abhinay Deo.

Asalin hoton, Alamy

Ciwon Ajali

A shekarar 2018, an gano cewar yana da ciwon daji da ya shafi kwayoyin halittarsa da ke fitar da sinadarai a cikin jini.

Ya wallafa wani sako a Twitter, yana cewa "Ba dole ne rayuwa ta ba mu abin da muke sa rai ba."

Ya nemi magani a London kuma ya wallafa wata kasida a shafinsa na Instagram da ke nuna cewa addininsa na taka muhimmiyar rawa a yadda ya karbi labarin cutar tasa.

"Allah na nuna mana alama kamar yadda ya halicce mu, sai ya tafi da mu sannu a hankali daga cikin duhu."