Coronavirus: Jihohi a Amurka sun fara bude harkokin kasuwanci

Amurka

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Wadanda cutar korona ta yi ajali a Amurka sun kai 51,000

Jihohi a Amurka sun fara bai wa wuraren kasuwanci damar budewa bayan dokokin da aka saka na dakile yaduwar cutar korona, yayin da wadanda suka mutu a kasar suka kai 51,000.

Shagunan gyaran gashi da na gyran jiki za su iya budewa a Jihar Georgia da Oklahoma, inda ita kuma Alaska ta dage wa wuraren cin abinci takunkumi.

A ranar Juma'a ne Shugaba Trump ya fice daga dakin taron manema labarai a lokacin da ba a saba gani ba, inda ya ki amsa tambayoyin 'yan jarida.

Shugaban ya sha suka bayan ya nuna cewa yi wa mutane allura da sinadarin wanke datti wato disinfectant zai iya taimakawa wurin maganin cutar.

Likitoci da masu kamfanonin samar da sinadarin sun yi watsi da kalaman nasa da cewa sinadarin yana da guba idan ya shiga cikin mutum, sannan idan ya taba jikin mutum zai iya yin illa ga fata da idanu da kuma huhu.

Sai dai a ranar Juma'a ya ce kalaman nasa, wadanda ya yi a ranar Alhamis, na ba'a ne kuma an yi masa gurguwar fahimta ne.

Kwastomomin da za su je shagunan kasuwancin ana sa ran za su ci gaba da bin shawarwarin bayar da tazara. Amma wasu yankunan sun zabi su ci gaba da zama a cikin kulle.