Najeriya za ta dauki mataki kan ‘yan ta’adda a Sokoto

'Yan bindiga a yankin Zamfara

Asalin hoton, Getty Images

Gwamnatin Najeriya ta ce ta shirya wani taro na musamman da masu ruwa da tsaki don tattaunawa kan here-hare a yankin Isa da Sabon Birni a jihar Sokoto.

Mai magana da yuwun shugaban kasar Malam Garba ne ya bayyanawa BBC haka ranar Asabar.

A daren Juma'a zuwa wayewar garin ranar ne wasu 'yan bindiga suka kai hari wasu kauyuka a yankin Sabon Birnin Gobir da ke jihar ta Sokoto inda suka kashe akalla mutum biyu, sannan suka jikkata wasu da dama.

Dan majalisar wakilai ta tarayya daga yankin Aminu Almustapha Bozo ya shaidawa BBC cewa ana yawan kai hare-hare a yankin a 'yan kwanakin nan.

Dan majalisar da ke wakiltar Sabon Birni ta Gabas ya ce sun jikkata wasu da dama tare da kwashe dukiyoyi da suka hada da dabbobi masu yawa.

"An harbi mutum uku, biyu sun mutu, daya yana kwance a asibitin Gidan Rumji a cikin Jamhuriyar Nijar," in ji Honarabul Aminu Almustapha Bozo.

Yankin na da bangare biyu ne, wani bangaren a cikin Nijar wani kuma a Najeriya, a cewar dan majalisar, kuma saboda sun fi kusa da Nijar shi ya sa aka kai wanda ya ji raunin can.

Ya kara da cewa babu jami'an tsaron Najeriya a yankin. Jami'an tsaron Nijar ne suka je wurin bayan harin na ranar Alhamis, a cewarsa.

Malam Garba Shehu ya ce gwamnati tana sane da karuwar hare-hare a yankin, kuma tana daukar matakai domin kawo karshensu.

Ya ce za a gudanar da wani taro ranar Talata mai zuwa wanda ministan tsaro zai jagoranta da nufin lalubo hanyar kawo karshen hare-haren.

Wadanda za su halarci taron a cewar Malam Garba sun hada da wasu 'yan siyasa daga yankin, da kuma shugabannin hukumomin tsaro na kasa.

Kakakin na na shugaban kasa ya ce gwamnati tana daukar matakai ciki har da kai far maki ta sama don dakile hare-haren da kuma farautar 'yan bindiga da ke addabar yankin.

'Yan bindiga masu fashin daji da satar mutane domin kudin fansa sun addabi yankin Zamfara inda ake tunanin sun fadada ayyukansu ne zuwa Sokoto da suke makwabtaka.