Boris Johnson: Budurwar Firai Ministan Burtaniya ta haifa masa ɗa

Boris Johnson and Carrie Symonds

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto,

Boris Johnson da Carrie Symonds lokacin da suka halarci coci a watan Maris

Firai Ministan Burtaniya, Boris Johnson da budurwarsa, Carrie Symonds sun sanar da samun haihuwar da namiji.

Mai magana da yawun Firai Ministan da abokiyar zamansa, ta ce uwar da danta duk suna cikin koshin lafiya.

Mista Johnson mai shekara 55 da Symonds mai shekara 32 sun sanar tun a watan Maris cewa suna sa ran samun da a farkon bazara, inda kuma aka yi musu baiko a karshen shekara.

Mista Johnson dai ya yi fama da cutar korona inda ya killace kansa na wasu 'yan makonni kafin daga bisani a kai shi bangaren kulawar gaggawa a asibiti lokacin da jikin nasa ya tsananta.

Daga karshe Boris Johnson ya warke daga cutar.

Firai Ministan dai ya kasance a asibitin Hukumar Lafiya Ta Burtaniya NHS tare da matarsa a lokacin haihuwar.

Mai magana da yawun nasa ta ce ''Firai Minista da Ms Symonds suna mika godiyarsu ga tawagar ungozomomi ta NHS.''

Mutanen biyu sun yi ta samun sakwannin taya murna daga 'yan siyasa, sannan mahaifin firai ministan Stanley ya ce ''ya yi matukar farin ciki'' da samun jika.

'Labari mai dadi'

A watan Maris ne Mr Johnson mai shekara 55 da Ms Symonds mai shekara 32 suka sanar da cewa suna tsammanin jariri a a farkon bazara, kuma an yi musu baiko a karshen shekarar da ta gabata.

Su ne na farko da suka tare a Fadar Downing ba tare da aure ba.

Jaririn shi ne da na farko ga Ms Symonds yayin da Mr Johnson kuwa ke da 'ya'ya biyar.

A ranar Litinin ne Mr Johnson ya koma bakin aiki bayan ya sha fama da jinyar cutar korona, inda har ya shafe kwana uku a dakin kulawa ta musamman ICU.

Ita ma budurwa tasa ta nuna alamun cutar.

A lokacin da yake ICU budurwa ta yi ta tura masa hotunan cikin jaririn don su debe masa kewa.

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto,

An taba yi wa Firai Minista Camerons ma haihuwa lokacin yana kan mulki a Fadar Downing Street a shekarar 2010

Sauran 'ya'ya hudun da Mr Johnson ya haifa tare da tsohuwar matarsa Barista Marina Wheeler, suna cikin shekarunsu na 20.

Rahotanni sun ce ya cimma yarjejeniyar saki da Ms Wheeler a watan Fabrairu.