Coronavirus: Babban likiti mai yaki da cutar a Legas shi ma ya kamu

Likitoci

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Jami'an lafiya da dama sun kamu da korona a Najeriya

Babban likitan cibiyar kula da masu dauke da cutar Korona da ke Yaba a Lagos ya kamu da cutar Covid 19.

BBC ta fahimci cewa Dr Bowale Abimbola wanda a yanzu haka yake cibiyar killace masu korona a Lagos, kawo yanzu dai yana fama da tari.

Bayanai sun ce yanzu mako guda kenan da likitan ya killace kansa.

Likitan na daga cikin ma'aikatar lafiya 113 da suka kamu da cutar Covid 19 a kokarinsu na dakile cutar.

Kawo yanzu an tabbatar da mutum 1,932 dauke da cutar korona a Najeriya a yayin da mutum 50 suka rasu sai kuma wasu 300 da suka warke.