Mace-macen Kano: Da alama coronavirus ce take kashen jama'a - Bincike

Makabarta

Wani bincike da wasu likitoci suka gudanar kan mace-macen da ake yi a Kano ya nuna cewa suna da dangantaka da cutar korona.

Masu binciken, wadanda wasu likitoci ne mata uku 'yan asalin jihar Kano sun ce sun dau aniyar binciken ne sakamakon rahotannin karuwar mace-macen da ake samu a birnin Kano a lokacin da ake fama da cutar korona.

Daya daga cikin masu bincikin Dakta Maryam Nasir Aliyu likita ce a Kano kuma tana koyarwa a Jami'ar Yusuf Maitama Sule a Kanon. Sauran kuma Dakta Zainab Mahmoud Dakta Khadija Rufa'i suna karatu ne da kuma aiki a Amurka.

Sun tattara bayanan binciken ne a cikin kwanaki biyu, inda suka tattauna da dangin mutum 183 da suka mutu a cikin kwaryar birinin Kano daga ranar 18 zuwa 25 ga watan Afrilun 2020.

Tun da farko dai sun shelanta daukar matakin a kafofin sada zumunta, inda suka nemi dangin wadanda suka mutu su tuntube su domin ba da bayanai.

Dakta Maryam ta shaida wa BBC cewa sun yi amfani ne da hanyar tattara bayanai ta yin hira da dangin mamatan, kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta zayyana.

Sakamakon binciken ya gano cewa kaso 96 cikin 100 na wadanda suka mutu din tsofaffi ne da suka haura shekara 60, sannan da damansu suna fama da cutuka kamar ciwon zuciya da hawan jini.

Binciken ya gano cewa, kaso 88 cikin 100 na wadanda suka mutu sun yi fama da zazzabi mai zafi.

Kaso 76 kuma sun yi fama da tari, yayin da kaso 80 kuma suka samu matsalar numfashi, har ta kai an sa wa wasu na'urar taimakawa wajen numfashi. Sannan kaso 39 sun yi fama da matsalolin ciki da suka hada da amai da gudawa da kuma cushewar ciki.

Haka kuma binciken ya gano cewa mutanen da suka mutu sun yi jinya ne ta tsawon kwanaki biyu zuwa kwana 14.

Dakta Maryam ta ce "Mafi yawan wadanda suka mutu din sun yi gajeriyar jinya ne, da ta zo da nau'in zazzabi wasunsu kuma da alamomi na mura."

"Gaskiya dai a ganinmu din akwai wadanda alamu ya nuna cewa akwai coronavirus," a cewar Data Maryam.

Sai dai ta ce ba za a yanke hukunci cewa cutar korona ba ce tun da ba a yi gwaji ba.

Ta kara da cewa daya daga cikin wadanda suka tattauna da su ya bayyana cewa mahaifinsa "ya fara da zazzabi, sannan kuma sai ya fara mura, sai ya fara tari ba kakkautawa, daga nan kuma sai numfashinsa ya fara sarkewa, har suka je asibiti aka saka masa iskar oxygine, sannan daga baya aka sa masa na'urar taimaka wa wajen numfashi."

Kalubale

Masu binciken sun ce babbar manufarsu ta gudanar da binciken ita ce gano musabbabin abinda ke yin ajalin mutane a Kano fiye da yadda aka saba gani.

Sai dai sun ce binciken nasu ya fuskanci kalubale da suka hada da cewar sun gudanar da binciken ne ta kiran wayar mutanen da ba a san su ba gabanin lokacin binciken.

Haka kuma wasu mutanen da aka kira sun ki bayar da bayanai kan mamatansu, yayin da wasu kuma ba sa bayar da sahihan bayanai.

Sannan kuma a cewarsu sun samu wasu bayanan da ba za su iya amfani da su ba, saboda wadanda suka bayar da bayanan ba su da alaka ta kusa da wadanda suka mutu din, don haka bayanansu ba za su zama sahihai ba.

Shawarwari

Masu binciken sun bayar da shawarwari shida, mafi yawancinsu ga hukumomi.

Tuni dai likitocin suka mika wannan rahoto ga gwamnatin jihar da nufin ba ta haske da taimaka mata wajen gano musabbabin mace-macen.

1. Gudanar bincike a kan kari kan mace-macen, ta hanyar tattara bayanai daga dangin mamatan, da masu kula da makabartu da kuma asibitoci.

2. Kara yadda ake gudanar da gwajin cutar korona a Kano, da samar da wuraren gwaji na tafi-da-gidanka kasancewar an kai matakin yaduwar cutar a cikin al'umma.

3. Samar da kayan kariya ga ma'aikatan lafiya musamman wadanda suke fara ganin marasa lafiya.

4. A lura cewa an yi watsi da wasu cutukan da jama'a ke fama da su, sannan a duba yiwuwar tura duk wanda ba ya fama da wasu cutukan da ba korona ba zuwa asibitoci masu zaman kansu da kuma kananan asibitoci.

5. A fitar da tsauraran ka'idoji wajen binne jama'a.

6. Bude muhimman wurare da kasuwannin sayar da abinci da magunguna.