Ina nan da raina ban mutu ba – Ghali Naabba

Ghali

Asalin hoton, Ghali Twitter

Tsohon shugaban majalisar wakilan Najeriya Ghali Umar Naabba ya musanta jita-jitar da ake yadawa a kafafen sada zumunta cewa ya rasu.

A wani hoton bidiyo da ya wallafa a shafukansa na Twitter da Instagram Ghali Naabba ya ce "Ina tabbatarwa da masoyana da kuma dukkan 'yan Najeriya da ma duniya gaba daya ma cewa ina nan lafiyata kalau da raina ban mutu ba"

A cikin bidiyon wanda ya nada cikin harshen Hausa da turancin Ingilishi ya ce abin takaici ne irin yadda ake yada wannan mummunan lanbari a kansa a 'yan kwanaki nan.

"A halin yanzu ina nan London, abinda ya kawo ni na gama yau sati uku ke nan ko hutu"

Ya ce rashin jirgi ne ma ya hana shi komwa Najeriya, sannan da zarar an samu hanya zai koma gida.

Ya ce yana so masoyansa da 'yan Najeriya baki daya su sani cewa, mutuwa na kan kowa kuma in tazo babu makawa sai an tafi.

A wannan makon nan ne aka fara yada jita-jitar cewa tsohon shugaban majalisar wakilan ya rasu, duk da cewa rahotanni sun bayyana cewa ba shi da wata rashin lafiya da ke damun shi.