Jimenez yana son komawa Madrid, Man Utd tana zawarcin Dembele

Raul Jimenez

Dan wasan Wolves Raul Jimenez, mai shekara 28, ya ce zai yi wahala ya ki amsa tayin komawa Real Madrid ko Barcelona, a cewar jaridar Express.

Jaridar Daily Star ta ce golan Manchester United Dean Henderson, mai shekara 23, wanda ya shafe kakar wasannin 2019-20 yana zaman aro a Sheffield United, yanzu ya shirya sake kashe wata shekarar ba tare da ya koma kungiyarsa ba.

Manchester United tana son dauko dan wasan Lyon Moussa Dembele, mai shekara 23, ko da yake kungiyoyin biyu basu tattauna a kan batun ba. (Manchester Evening News)

Dan wasan Chelsea Willian, mai shekara 31, ya ce ba laifi ba ne idan ya koma wata kungiyar a London - inda aka ce zai koma Tottenham ko Arsenal. (Desimpedidos - Brazilian, via Mirror)

Dan wasan Bournemouth Ryan Fraser, mai shekara 26, ya shaida wa abokansa cewa yana son komawa Tottenham a bazara idan kungiyar ta yi zawarcinsa, in ji jaridar Football Insider.

Independent ta rawaito cewa dan wasan Atletico Madrid Hector Herrera, mai shekara 30, yana cikin 'yan wasan da West Ham ta so daukowa lokacin musayar 'yan kwallon kafa a watan Janairun da ya wuce, kuma kungiyar za ta sake yunkurin dauko shi.

Jose Luis Gaya ya bai wa takwaransa dan wasan Valencia Ferran Torres, mai shekara 20, shawarar cewa kada ya koma Liverpool. (Marca - Spanish, via Liverpool Echo)

Kocin Leicester City Brendan Rodgers, ya ce kasafin kudin da suka yi a bana ba zai iya sayo musu dan wasan Barcelona Philippe Coutinho, mai shekara 27 ba, duk da rade radin da ake yi cewa kungiyar za ta dauko dan wasan na Brazil. (Leicester Mercury)

Sabon dan wasan Watford Pape Gueye, mai shekara 21, ba ya son murza leda a kungiyar duk da kwangilar shekara biyar da ya sanyawa hannu saboda yana tsoron za ta bayar da aronsa. (Radio France)

Liverpool ta tuntubi dan wasan Napoli Kalidou Koulibaly, mai shekara 28, a matsayin dan wasan da take so ya maye gurbin Joel Matip. (Tutto Mercato - Italian)