Coronavirus: Cutar ta kashe likita daya, ta kama 34 a Kano

Corona

Asalin hoton, Getty Images

Kungiyar likitoci ta Najeriya reshen jihar Kano ta tabbatar wa BBC mutuwar likita daya a jihar, yayin da 34 da sauran ma'aikatan lafiya suka kamu da cutar korona.

Shugaban kungiyar likitocin na jihar Kano ne, Dr Sanusi Muhammad Bala ya ce "a yanzu dai alkaluman da muke da su daga asibitoci guda shida da ke birnin na nuna muna da mutum 34 da suka kamu da cutar, inda mutum daya ya rasu."

Ya kara da cewa sai dai an samar da kayan kariya a asibitoci amma kuma ba zan iya ba ka bayani ba kasancewar yanzu muke karbar rahotanni.

Kafin wannan sanarwa wani jami'i a asibitin koyarwa na Aminu Kano da ke birnin Kano, ya tabbatar wa BBC cewa mutum 10 ne suka kamu da cutar a asibitin.

Inda ya ce ma'aikatan sun kamu da cutar ne sakamakon duba wasu marasa lafiya da suka je asibitin da wata cutar daban amma daga bisani sai aka fahimci suna dauke da cutar korona, al'amarin da ya sa ma'aikatan asibitin suka harbu.

Ko a makon da ya gabata ma an samu rahotannin da ke cewa ma'aikatan asibitin fiye da 10 su ma sun kamu da cutar ta korona ta irin wannan hanya.

Bayanai dai na nuna cewa likitoci a Kano sun rika guje wa marasa lafiya saboda tsoron abin da ka iya faruwa.

A kwanakin baya dai likitocin sun koka da rashin kayan aiki da ya kamata su sanya a yanayin annoba irin ta korona.

Ko a lokacin da cutar zazzabin Lassa ta bulla a birnin na Kano sai da ta yi ajalin likitoci guda biyu.