Kwamishinan da Ganduje ya tuɓe 'ya kamu da cutar korona'

Muaz Magaji

Asalin hoton, Muaz Magaji

Tsohon kwamishinan ayyukan jihar Kano da ke Najeriya, wanda Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya tube sakamakon 'yin murna' da mutuwar shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar, Abba Kyari, ya ce ya kamu da cutar korona.

A waki sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Alhamis, Injiniya Mu'azu Magaji, ya ce yanzu haka yana cibiyar killace masu dauke da cutar korona a ke Kano.

A cewarsa, "Da safiyar nan sakamakon gwajin da hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta yi min ya fito. An tabbatar ina dauke da Covid-19... kuma an kai ni cibiyar kula da masu dauke da cutar. A taya ni da addu'a.

Asalin hoton, Facebook/Muaz Magaji

A watan jiya ne Injiniya Mu'azu Magaji ya janyo ce-ce-ku-ce a Najeriya bayan ya yi kalaman da wasu ke gani na nuna murna ne da rasuwar Abba Kyari, wanda ya mutu sakamakon kamuwa da cutar korona.

Sai dai kwamishinan -- wanda bai musanta cewa ba shi ya wallafa bayanan ba -- ya yi nadama a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce rashin fahimtar bayanan da ya wallafa a Facebook aka yi, har ta kai ga daukar matakin tube shi daga mukaminsa na kwamishina.

"Ina neman gafara ga duk wani abin da ya haifar da rudani, da martani, dukkaninmu muna cikin mawuyacin lokaci na damuwa inda damuwa da kunci ke sa da wahala a iya bambance fahimta da rashin fahimta."

"Na yi nadama kan duk wani bakin ciki da na janyo wa iyalan marigayi shugaban ma'aikata a fadar shugaban kasa da kuma maigida na Gwamna Abdullahi Umar Ganduje," a cewar tsohon kwamishinan.